Yan Ta'adda sun Mamaye Fitaccen Gari a Zamfara, 'Dan Majalisa ya Nemi Dauki

Yan Ta'adda sun Mamaye Fitaccen Gari a Zamfara, 'Dan Majalisa ya Nemi Dauki

  • Yayin da aka kammala taron yadda za a shawo kan matsalolin tsaro a jihohin Arewa maso Yamma a Katsina, dan majalisa a Zamfara ya koka
  • 'Dan majalisa, Rilwanu Marafa Na Gambo ya ce yan ta'adda na kashe jama'arsa babu dare babu rana, kuma su yi tafiyarsu ba tare da an kama su ba
  • Na Gambo ya roki gwamnan Dauda Lawal Dare da ya gaggauta kawo masu dauki domin dakile hare-haren da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Zamfara- Dan majalisa a jihar Zamfara, Rilwanu Marafa Na Gambo, ya nemi tallafin gwamna Dauda Lawal Dare kan a gaggauta shawo kan rashin tsaron da ya addabi yankinsa.

Kara karanta wannan

Aure mai dadi: Mawaki Davido gwangwaje amaryarsa da kyautar motar alfarma

Dan majalisar ya shaidawa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar cewa yan ta’adda na cin karensu babu babbaka yayin da suka hana mutanen karamar hukumar Anka sakat.

Zamfara
Dan majalisa a Zamfara ya koka kan rashin tsaro Hoto; Legit.ng
Asali: Original

Daily Trust ta wallafa cewa a kullum sai yan bindiga sun kashe mutanensa, yayin da su ke sace wadansu daga cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘”Yan ta’adda sun mamaye Anka,” Dan majalisar Zamfara

Dan majalisa a jihar Zamfara, Rilwanu Marafa Na Gambo, ya bayyana cewa yan ta’adda sun mamaye da yawa daga mazabun da ke karamar hukumar Anka.

Rilwanu Marafa Na Gambo ya ce yan bindiga sun mamaye mazabu bakwai daga cikin 10 da ke karamar hukumar inda su ke ta’addancinsu.

Ya ce da yawa daga mazauna yankin sun bar gidajensu da gonakinsu saboda matsa masu da hare-hare da ‘yan bindigar su ka yi ba dare ba rana.

Yan bindiga sun kai mummunan hari masallaci

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

A baya kun ji cewa wasu yan ta'adda sun kai mummunan hari kauyen Tazame da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara inda su ka kashe mutane da dama.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da harin da ya salwantar da ladanin masallacin da ganinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.