Bola Tinubu Yana Jagorantar Taron FEC a Fadar Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa (FEC) a fadar gwamnatinsa da ke birnin tarayya Abuja
- Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila sun halarci taron
- Wannan zama na zuwa ne mako shida bayan taron yini biyu da FEC ta yi a watan jiya, wanda aka amince da tsare-tsare da ayyuka 20
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) yanzu haka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Taron na gudana ne a ɗakin taron majalisar da ke fadar gwamnatin Najeriya yau Talata, 25 ga watan Yuni, 2024.
Majalisar FEC ta zauna bayan makonni
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, taron FEC na yau na zuwa ne bayan wanda aka yi kwana biyu ana yi kusan makonni shida da suka gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaman FEC na ƙarshe. gwamnatin Bola Tinubu ta amince da ayyuka daban-daban har guda 20.
Galibin ministoci sun halarci taron FEC
Waɗanda suka halarci taron da ke gudana yanzu haka sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Femi Gbajabiamila.
Bugu da ƙari, an tattaro cewa mafi akasarin ministocin Bola Tinubu sun halarci taron majalisar a wannan karon, rahoton Leadership.
Canza ranar zaman majalisar FEC
Idan za ku iya tunawa Shugaba Tinubu ya kaddamar da majalisar ne ranar 28 ga watan Augusta, 2023 kuma ya sauya ranakun taron daga Laraba zuwa Litinin a kowane mako.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, a ranar 16 ga Oktoba, 2023, ya bayyana cewa majalisar za ta rika zama ne idan akwai muhimman batutuwan da za a duba.
"Saboda haka daga yanzu taron FEC ya koma ranakun Laraba kuma ba lallai ne kowane mako za a yi taron ba, idan babu batun da za a tattauna, za a ɗaga zuwa mako na gaba."
Tinubu ya naɗa shugaban FCCPC
A wani labarin na daban Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mr. Olatunji Bello a matsayin shugaban hukumar FCCPC ta ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya tabbatar da wannan naɗi a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng