Ana Shirin Naɗa Sabon Sarki, Gwamna Ya Yi Sauye Sauye Masu Muhimmanci

Ana Shirin Naɗa Sabon Sarki, Gwamna Ya Yi Sauye Sauye Masu Muhimmanci

  • Gwamna Seyi Makinde ya yi garambawul a majalisar zartarwar jihar Oyo, ya sauya wa wasu kwamishinoni wurin aiki
  • Makinde ya canja kwamishinonin ma'aikatar kananan hukumomi da masarautun Oyo, da wasu ma'aikatu a gwamnatinsa
  • Wannan sauye-sauye zai fara aiki ne nan take kuma ya yi haka ne domin kara inganta ayyukan gwamnati da kafa shugabanci nagari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi wani ɗan karamin garambawul a majalisar zartaswan jiharsa.

Gwamnan ya sauyawa wasu kwamishinoni wuraren aiki domin inganta ayyukan gwamnatinsa da kuma ƙoƙarin cika muradan al'ummar jihar Oyo.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamna Makinde ya yi gyare-gyare a majalisar zartarwa ta jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Gwamna Makinde ya yi garambawul

Daga cikin sauye-sauyen da gwamnan ya yi, tsohon kwamishinan kasuwanci, masana'antu da zuba jari, Ademola Ojo ya koma ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Mista Ojo ya kasance tsohon shugaban ma'aikatan ƙananan hukumomi reshen jihar Oyo.

Honorabul Segun Olayiwola, wanda kafin wannan lokaci shi ke riƙe da ma'aikatar kananan hukumomi, a yanzu Makinde ya mayar da shi ma'aikatar bayar da horo.

Tsohon kwamishinan ma'aikatar Adeniyi Adebisi, zai koma ma’aikatar kasuwanci, masana’antu, da zuba hannun jari.

Wannan sauye-sauye da Mai Girma Gwamna Makinde ya yi zai fara aiki ne nan take, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito rana Talata, 25 ga watan Yuni, 2024.

Gwamnan Oyo ya naɗa Olubadans

Wannan na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan Gwamna Makinde ya amince da naɗin Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon sarkin Ibadan watau Olubadan.

Seyi Makinde ya amince da naɗin sabon sarkin mai daraja biyo bayan shawarin da ya karɓa daga majalisar masu naɗa sarki a masarautar.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

Hakan ya biyo bayan rasuwar tsohon Olubadan, Oba Balogun, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa ranar 14 ga watan Maris, 2024.

Bola Tinubu ya yabawa gwamna Makinde

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohin ƙasar nan su yi koyi da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta ya ce jikoki masu tasowa ba za su manta da Gwamna Makinde ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262