Abba Gida Gida Zai Gwangwaje Manoman Kano da Taki, Za a Kashe N5bn Kan Tallafi

Abba Gida Gida Zai Gwangwaje Manoman Kano da Taki, Za a Kashe N5bn Kan Tallafi

  • Gwamnatin jihar Kano ta fitar da Naira biliyan 5.07 domin sayen taki tare da raba shi ga ƙananan manoman jihar a daminar shekarar 2024
  • Gwamna Abba Yusuf ya ba da umarnin sayo takin a taron majalisar zartarwar jihar na 15, kamar yadda kakakinsa, Sanusi Dawakin Tofa ya sanar
  • Sanusi D/Tofa ya ce ba manoma tallafin takin zai taimaka wajen bunƙasa harkar noma da kuma tabbatar da wadatuwar abinci a fadin jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya amince da sayen takin noma na Naira biliyan 5.07 domin tallafawa kananun manona a jihar.

Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Kano take dauka na bunƙasa harkar noma da kuma tabbatar da wadatuwar abinci a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware N1bn domin muhimman ayyuka a bangaren lafiya

Gwamnatin Kano ta yi magana kan noman 2024
Gwamna Abba Yusuf zai ba manoman Kano tallafin taki. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Tofa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Abba za ta rabawa manoma taki

Sanusi D/Tofa ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ya amince a fitar da kudin tare da sayo takin ne a yayin da ya jagoranci taron majalisar zartarwar jihar na 15.

A cewar sanarwar:

"Za a raba takin ne zuwa ga kananan hukumomi 44 na jihar domin tallafawa manoma, musamman wadanda suke a karkara.
"Manufar ba da tallafin ita ce samar da wadataccen amfanin gona a daminar 2024, wanda zai kai ga bunkasa aikin noman."

A cewarsa, za a sayarwa manoman takin a farashi mai rahusa, wanda ke alamta kudurin gwamnan na ganin al'ummar jihar sun yi noma cikin sauki.

Gwamna Abba ya rabawa talakawa hatsi

Kara karanta wannan

Rusa fadar Nasarawa: Gwamnatin Abba ta ba Aminu Bayero sabon umarni a Kano

Bisa ga damuwa da tsadar da kayan abinci suka yi, Sanusi Tofa ya ce Gwamna Abba ya sayo hatsi na biliyoyin Naira tare da raba ma talakawan jihar domin saukaka masu.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan jihar a lokuta da dama na nuna dagewarsa kan samar da abinci da kuma tallafawa manoman Kano.

Sanusi Bature ya ce dukkanin abin da gwamnan yake yi yana daga cikin alkawuran da ya daukarwa al'ummar Kano a lokacin yakin zaben 2023.

Gwamnatin Kano za ta gyara fadar Nasarawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta bayyana cewa za ta gyara wasu ɓangarori na fadar Nasarawa da ke kwaryar Kano ba tare da bata lokaci ba.

Gwamna Abba Yusuf ya ba kwamishinan 'yan sandan jihar umarnin ya fitar da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga karamar fadar domin ba shi damar yin gyare-gyaren.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.