Ana Jita Jitar Tsige Sarkin Musulmi, Atiku Ya Ba da Shawara 1 Ta Kare Martabar Sarakuna

Ana Jita Jitar Tsige Sarkin Musulmi, Atiku Ya Ba da Shawara 1 Ta Kare Martabar Sarakuna

  • Dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi kira da a sanya masarautu a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Atiku Abubakar ya ce hakan ne zai kare masarautu daga barazanar rugujewa saboda katsalandan da gwamnoni ke yi wa sarakuna
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi kira ga gwamnoni da su mutunta sarakuna, yayin da ya bayyana muhimmancin masarautu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda gwamnoni ke taɓa rawunan sarakunan gargajiya a jihohinsu.

Atiku Abubakar ya ce abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan na tsige sarakuna a jihohi ya fara zama tamkar cin fuska ga sarautun gargajiya.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Bayero: Manazarci ya hango makomar sarautar Kano bayan hukuncin kotu

Atiku ya yi magana kan martabar sarakuna
Atiku ya ba da shawarar kare martabar sarakunan Najeriya. Hoto: @atiku
Asali: Getty Images

Dan takarar shugaban kasa karkashin PDP a 2023, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A kare sarakuna daga gwamnoni" - Atiku

Atiku Abubakar ya ce duk da cewa masarautun gargajiya na karkashin kulawar kananan hukumomi, ya zama wajibi a rika kallonsu matsayin ginshikin da ya gina tsarin mulki.

Da wannan, Atiku ya ke ganin ya zama dole a kare masarautu daga gwamnatin jihohi musamman wadanda ke kokarin rusa tsarin gudanarwarsu.

Atiku ya ce:

"Idan har babu daidaito a tsarin gudanarwar sarakunanmu na gargajiya, hakan zai kawo cikas ga daidaita zaman lafiya da kwanciyar hankali a garuruwa."

"A saka masarautu a dokar ƙasa" - Atiku

A yayin da yake magana kan hanyoyin kare masarautu a Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

"A wannan gabar, ina mai yin kira da a sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar nan domin sanya masarautu a cikin doka da kuma tsara gudanarwarsu.
"Wannan garambawul din zai kara taimakawa wajen dakile ta'addanci da kuma tabbatuwar tsaro a garuruwan ƙasar."

Atiku ya nemi gwamnoni su girmama sarakuna

Atiku Abubakar ya ci gaba da cewa:

"Duk da cewa babu masarautu a cikin dokar kasarmu, sai dai abu ne a fili cewa sarakuna na taka rawa wajen ci gaban kasa da kuma wanzar da zaman lafiya.
"Masarautu na taimakawa wajen jagorantar jama'a, don haka dole ne mu kare martabarsu ba wai mu rusa su ba.
"Ina kira ga gwamnonin jihohi da su girmama sarakunan gargajiya. Jagorancin da sarakuna ke yi shi ke nuna ainihin al'adun mu tun na kaka da kakanni."

Gwamnan Sokoto zai tsige Sarkin Musulmi?

Wannan dai na zuwa ne awanni bayan da kungiyar MURIC ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Sokoto na shirin tsige Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar.

Kara karanta wannan

Gaisuwar Sallah ko shirin zaben 2027? Shugabannin Najeriya 3 da Atiku ya ziyarta

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin inda ya gargadi gwamnan jihar kan wargi da kujerar sarkin.

Gwamna ya ba Aminu umarnin barin fada

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake aika sakon umarni ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan zamansa fadar Nasarawa.

Gwamnatin Kano ta umarci Aminu Bayero da ya gaggauta ficewa daga fadar Nasarawa domin ba ta damar gudanar da gyare-gyaren da ta shirya yi a karamar fadar sarkin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel