Sarkin Musulmi Ya Fadi Lokacin da Za a Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro a Arewa

Sarkin Musulmi Ya Fadi Lokacin da Za a Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro a Arewa

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa za a ɗauki shekaru masu yawa kafin a kawo ƙarshen ƴan bindiga a yankin
  • Ya nuna cewa a shirye sarakunan gargajiya suke wajen haɗa kai da jami'an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar da ta daɗe tana ciwa mutanen yankin tuwo a ƙwarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Sarkin Musulmi, Muhammadu Saad Abubakar III, ya yi magana kan matsalar ƴan bindiga da ta addabi yankin Arewa maso Yamma.

Sarkin Musulmin ya ce za a ɗauki shekaru masu yawa kafin yankin ya magance matsalar rashin tsaron da yake fama da ita.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari kan bayin Allah, sun kashe rayuka da yawa a Arewa

Sarkin Musulmi ya yi magana kan rashin tsaro
Sarkin Musulmi ya nuna damuwa kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Tashar Channels tv ta ce shugaban majalisar ƙolin harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya bayyana hakan ne a wajen taron zaman lafiya da tsaro na yankin Arewa maso Yamma da aka gudanar a jihar Katsina ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi a kan rashin tsaro

"Abin da ya kamata mu yi shi ne mu ƙalubalanci waɗannan ƴan bindigan saboda mun san illar ayyukan ƴan bindiga da masu tayar da ƙayar baya a rayuwarmu."
"Amma zai ɗauki shekaru kafin mu kawo ƙarshen matsalar idan har za mu ga ƙarshen ta. Mun san dukkanin abin da take haifarwa da matsalolin."

- Muhammad Sa'ad Abubakar

Sarkin Musulmin ya nuna cewa a shirye sarakunan gargajiya suke wajen haɗa kai da jami'an tsaro da gwamnoni bakwai na yankin domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a yankin.

An yi taro kan rashin tsaro a Katsina

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarauta a Kano, wani gwamna ya rage wa sarakuna ƙarfin iko

Ya yi amanna cewa a ƙarshen taron, za a samar da mafita wajen kawo ƙarshen matsalar ta yadda mutane za su koma rayuwarsu cikin walwala.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sauran sun haɗa da gwamnoni bakwai na yankin Arewa maso Yamma, hafsoshin tsaro da sufeta janar na ƴan sanda.

Batun tsige Sarkin Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi (MURIC) ta koka kan shirin da Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sokoto yake yi na tsige Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Shugaban ƙungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola a cikin wata sanarwa da ya fitar ya gargadi gwamnan da kada ya yi wargi ga kujerar Sarkin Musulmin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel