Kungiyar MURIC Ta Fallasa Shirin da Ake Yi Kan Sarkin Musulmi, Ta Yi Gargadi

Kungiyar MURIC Ta Fallasa Shirin da Ake Yi Kan Sarkin Musulmi, Ta Yi Gargadi

  • Ƙungiyar MURIC ta yi zargin cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu na shirin tsige Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III
  • Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 24 ga watan Yunin 2024
  • Farfesan ya gargaɗi gwamnan da ya guji wargi da kujerar Sarkin Musulmin domin gujewa fuskantar fushin al'ummar mabiya addinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi (MURIC) ta koka kan shirin da Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sokoto yake yi na tsige Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Babban daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Nasir El-Rufai ya ziyarci Buhari a Daura, hotuna sun bayyana

MURIC ta yi zargin ana shirin tsige Sarkin Musulmi
Kungiyar MURIC ta zargi gwamnan Sokoto da shirin tsige Sarkin Musulmi Hoto: Muhammad Sa'ad Abubakar III, Sokoto State Government
Asali: Facebook

Sanarwar da aka sanya a shafin yanar gizon hukumar ta yi gargaɗi ga Gwamnan da kada ya taɓa kujerar Mai alfarma Sarkin Musulmi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi: Wane gargaɗi MURIC ta yi?

A cikin sanarwar, Akintola ya ce Musulmin Najeriya ba za su amince da duk wani tunanin tsige Sarkin Musulmi ba.

"Abin da bayanai suke nunawa shi ne gwamnan na iya komawa kan Sarkin Musulmi a kowane lokaci daga yanzu ta hanyar amfani da uzurin da ya kawo wajen tsige sarakunan gargajiya 15 da ya yi."
“MURIC na shawartar gwamnan da ya yi taka tsan-tsan. Kujerar Sarkin Musulmi ba kawai ta gargajiya ba ce. Kujera ce ta addini."
"Haka kuma ikonsa ya wuce Sokoto. Ya shafi dukkanin Najeriya. Shi ne shugaban al'ummar Musulmin Najeriya."
"Saboda haka duk wani gwamna da ya yi wargi ga kujerar Sarkin Musulmi zai fuskanci fushi daga al'ummar Musulmi, saboda kujerar na da matsayin Sarkin Musulmi da shugaban majalisar NSCIA."

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki tsattsauran mataki kan masallatai da coci a Plateau, ya kakaba doka

- Farfesa Ishaq Akintola

Shugaban na MURIC ya gargaɗi Gwamna Ahmed Aliyu da ka da ya fusata al'ummar Musulmi su ɗauki mataki mai tsauri.

Sarkin Musulmi ya yi kira ga shugabanni

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya tunatar da shugabanni kan halin tsadar rayuwa da ake ciki.

Sarkin Musulmin ya yi kira ga shugabannin a dukkanin matakai da su ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng