Abin da Ke Faruwa a Kano: ’Yan Sanda Sun Mamaye Fadar Mai Martaba Sarki Sanusi II
- Jami'an rundunar 'yan sanda sun mamaye fadar Sarkin Kano, inda Muhammadu Sanusi II yake zama, kamar yadda rahotanni suka bayyana
- An ruwaito cewa 'yan sandan sun fara fatattakar 'yan tauri da ke gadin Sarki Sanusi II daga fadar, kafin suka mamaye ta gaba daya
- Ana zargin cewa, an kori 'yan taurin ne a wani yunkuri na dawo da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero fadar sarki bayan hukuncin kotu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sanda sun dura fadar Sarkin Kano, sun tarwatsa 'yan taurin da ke gadin Sarki Muhammadu Sanusi II.
Bayan fatattakar 'yan taurin, an ce jami'an 'yan sandan sun kuma mamaye fadar gaba daya.
'Yan sanda sun mamaye fadar sarkin Kano
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, 'yan taurin sun kama gabansu jim kadan bayan da jami'an 'yan sandan suka mamaye fadar sarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce an ɗauko 'yan taurin ne daga sassa daban-daban na jihar Kano, domin su yi gadin Muhammadu Sanusi II tun bayan da aka naɗa shi sarki.
Sai dai rahoton ya ce an kori 'yan taurin ne a wani yunkuri da ake zargin gwamnatin tarayya na yi na mayar da Aminu Bayero babbar fadar masarautar.
Umarnin kotu da na Abba Yusuf
Wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Abba Yusuf ya ba da umarnin a gaggauta rusa katanga da wasu sassa na fadar Nasarawa domin yin gyare-gyare.
Sai dai 'yan sanda sun yi martanin cewa ba za su bi umarnin gwamnan jihar ba kan fitar da Aminu Bayero daga fadar, saboda umarnin babbar kotun tarayya da ta dakatar da hakan.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa ana ƙoƙarin a mayar da Aminu Bayero fadar sarki ne biyo bayan wani hukuncin babbar kotun tarayya da ya ƙalubalanci tsige shi.
Kotu ta rusa tsarin soke dokar masarauta
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai Shari'a Muhammad Liman na babbar kotun tarayya da ke da zama a Kano ya rusa tsarin da aka bi wajen soke dokar masarautun Kano ta 2019.
Alkalin kotun, ya ce wadanda ake karar suna sane da umarnin da kotun ta bayar a lokacin da ta rusa dokar, amma ta yi gaban kanta ta aiwatar da dokar duk da an hanata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng