Matsin Rayuwa: Rahoton CBN Ya Nuna Yadda 'Yan Najeriya Suka Koma Lafto Bashi

Matsin Rayuwa: Rahoton CBN Ya Nuna Yadda 'Yan Najeriya Suka Koma Lafto Bashi

  • Da alama matsin rayuwa da rashin isassun kudi a hannun jama'ar kasar nan ya sanya su juyawa kan karbar basussuka domin gudanar da rayuwarsu ta yau da gobe
  • Rahoton babban bankin kasa (CBN) ya fitar ya nuna cewa an samu karuwar bashin da 'yan Najeriya su ka karba a watan Janairu da 12% idan aka kwatanta da Disamban 2023
  • Rahoton ya kara da cewa yanzu haka bashin da ake bin 'yan Najeriya ya hau zuwa N3,028bn yayin da bankin CBN ya kara kudin ruwa kan rancen kudi da 26.95% a watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Yayin da rayuwa ke kara tsada, wani rahoton CBN ya gano yadda al'umma ke kara karbar rance domin gudanar da rayuwa ta yau da kullum.

Kara karanta wannan

'Bashi bai amfanar talaka', an bukaci binciken yadda Najeriya ke kashe bashin da ta ci

Rahoton ya gano cewa an samu karuwar rancen da 'yan Najeriya su ka karbo da 12%, inda a watan Janairu aka samu karuwar kudin zuwa N3.9bn.

Rance
Matsin rayuwa ya haddasa karuwar rancen kudi a Najeriya Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Channels Television ta wallafa cewa an samu karuwar rancen kudin da mutane su ka yi na amfanin kansu da 14.3%, wanda ya kai N3.028bn daga N2.649bn da aka karba a Disambar 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Najeriya na karbar bashi ta intanet

Rahoton ya bankado yadda bashin amfanin kaya na da za a sayar ya karu da 4% inda kudin ya kai N795bn, amma an samu raguwar bashin da ake karba ta kafar intanet da 1%.

Western Post ta wallafa cewa alkaluman da hukumar kididdiga ta bayyana samun hauhawar farashi da 33.95%, wanda ya tilastawa babban bankin kasa (CBN) kara kudin ruwa da 26.95%.

Wani bincike da SBM ya yi ya gano cewa 27% na 'yan Najeriya sun koma karbar bashi ta mahajojin bayar da bashi na yanar gizo domin iya gudanar da rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Kwalara na kisa a awanni, gwamnatin Kano ta yi gargadin amfani da ruwan sama

Shugaban kasa zai karbo sabon bashi

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin karbo sabon bashin Dala Biliyan 2.25 daga bankin duniya domin gudanar da wasu ayyuka a kasar nan.

Ministan kudi, Wale Edun da ya tabbatar da kokarin karbo bashin ya ce kudin ya na da saukin ruwa, kuma Najeriya za ta biya a hankali cikin shekaru 40.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.