An Shiga Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Kama Gadan Gadan a Babbar Cocin Najeriya
- Gobara ta tashi a gadan gadan a hedikwatar cocin Christ Embassy dake Ikeja, Legas a safiyar Lahadi, 23 ga watan Yuni
- Hukumar kashe gobara ta jihar Legas (LSFRS) ta bayyana cewa gobarar ta kama babban dakin taro na cocin kuma ta yi barna
- Legit Hausa ta ci karo da wani faifan bidiyo a intanet wanda ya nuna yadda gobarar ta ke ci tare da fitar da bakin hayaki a rufin majami'ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ikeja, jihar Legas – Gobara ta tashi a gadan gadan a hedikwatar cocin Christ Embassy, dake unguwar Oregun a Ikeja, jihar Legas.
An tattaro cewa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas sun dukufa wajen kashe wutar da ta tashi, kuma sun fitar da jawabi.
Gobara ta babbake cocin Christ Embassy
Wani mai amfani da shafin X (wanda aka fi sani da Twitter) @Chief_Augustin1 ya wallafa bidiyon gobarar a ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Augustine ya ce ba a fara gabatar da ayyukan ibada na ranar Lahadi ba a lokacin da gobarar ta tashi.
“Cocin Christ Embassy da ke kan titin Billingways, a Oregun ya kama da wuta. Jami'an hukumar kashe gobara ta Legas suna bakin kokarinsu wajen ganin an kashe ta."
Kalli bidiyon gobarar nan kasa:
Hukumar LSFRS ta fitar da rahoto
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas (LSFRS) ta ce an shawo kan gobarar da ta kama babban dakin taro na hedikwatar Christ Embassy in ji jaridar Premium Times.
Daraktar LSFRS, Margret Adeseye, ta tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Legas.
Ta ce gobarar ta ta'azzara ne saboda jami'an kashe gobara na cocin sun yi tunanin za su iya magance lamarin ba tare da tuntubar hukumar kashe gobara ta Legas ba.
Jaridar The Punch ta wallafa karin bidiyo kan barnar da gobarar ta yi.
Hajj: Jirgin Alhazan Najeriya ya iso gida
A wani labarin, mun ruwaito cewa kashi na farko na alhazai 410 daga jihar Kebbi da suka yi aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya sun dawo gida.
Jirgin farko na alhazan Najeriya da ya iso gida ne da misalin karfe 9:42 na yammacin ranar Asabar a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi.
Asali: Legit.ng