Wuta ta yi barna yayin da gobara ta lamushe dukiya a Garin Gwalameji
Wani ‘dan jarida da ke aiki da hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, mai suna Abdul-Saheed Olaide, da wasu mawakbtansa sun rasa dukiyarsu a wata wuta da ta barke a gidansa a Bauchi.
Wannan Bawan Allah da ke zaune a wani Gari na Gwalameji da ke jihar Bauchi da wasu mutanen sun gamu da wannan annoba ne a yammacin jiya Ranar Lahadi, 24 ga Watan Nuwamban 2019.
Sauran wadanda wannan gobara ta yi wa ta’adi sun hada da wani Ma’aikacin jaridar The Nation mai suna, David Adenuga. Wutar ta fara ci ne da kimanin karfe 1:30 na rana daga cikin wani jeji.
Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Premium Times, wannan gobarar ba ta bar wasu ‘Daliban makarantar koyon aikin nan da ke Garin Bauchi ba bayan da ta kona dakuna akalla tara.
Abdul-Saheed Olaide ya bayyanawa Manema labarai cewa gobarar ta ci kayan aikinsa da sauran dukiya barkatai da bai ambata ba. Duk da haka ya godewa Ubangiji da ya samu ya tsira da ransa.
KU KARANTA: El-Rufai zai rusa fitacciyar gadar da ke Garin Kaduna
Shi ma Mista Adenuga ya ce gobarar ta zo masa nema kamar a mafarki inda fadawa ‘yan jarida ya rasa komai. “Abin kamar mafarki. Komai da ya ke cikin daki na a da, yanzu wuta ta cinye shi.”
“Babu lantarki a lokacin; har yanzu ba mu san daga inda wutan ta taso ba. Gobarar ta ci dakuna tara. Sai da ‘yan kwana-kwana su ka zo sannan aka iya kashe ta bayan ta ci wasu dakunan.”
Adenuga ya kara da cewa daga cikin abubuwan da ya rasa har da takardun shaidar karatunsa. “Yanzu ban ma san ta ina zan fara ba. Abin da su ka rage mani kurum su ne kayan da ke jiki na.
Musa Sule ya shaidawa ‘yan jarida cewa gobarar ta ci dakunan Unguwar Tinubu Lodge. Wata ‘Daliba mai suna Goodness Okpara ta ce ta na coci abin ya faru, amma sun tsira da wasu kayan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng