Sanusi II vs Aminu: Lauya Ya Fadawa Abba Yadda Zai Kawo Karshen Rikicin Sarautar Kano

Sanusi II vs Aminu: Lauya Ya Fadawa Abba Yadda Zai Kawo Karshen Rikicin Sarautar Kano

  • Fitaccen lauya, Inibehe Effiong, ya mayar da martani kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke kan rikicin masarautar Kano
  • Barista Effiong ya ce hukuncin da Mai shari’a Muhammad Liman ya yanke bai warware batun ba sai dai ya kara dagula al'amura
  • A wata zantawarsa da Legit.ng, lauyan ya ce gwamnan Kano na iya kawo ƙarshen rigimar ta hanyar soke majalisar masarautar gaba daya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano – Barista Inibehe Effiong ya ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke ya kara dagula batun rikicin masarautar Kano tsakanin Sarki Sanusi II da Aminu Bayero.

Barista Effiong ya ce akwai rudani a hukuncin da mai shari’a Muhammad Liman ya yanke a ranar Alhamis, 20 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Babban lauya ya bayyana sahihin Sarkin Kano

Fitaccen lauya ya yi martani gme da hukuncin da kotu ta yanke kan rikicin masarautar Kano
Barista Effiong ya ce hukuncin babbar kotun tarayya ya kara dagula al’amura a Kano. Hoto: @Adam_L_Sanusi/@Engr_Alkasimfge/@InibeheEffiong
Asali: Twitter

Lauyan ya ce a bangare daya, hukuncin ya kiyaye martabar doka, amma a daya bangaren kuma ya rusa ayyukan Gwamna Abba Yusuf wanda shi ma ya bi doka wajen nada Sarki Sanusi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan rajin kare hakkin dan Adam din ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Asabar, 22 ga watan Yuni.

"Hukuncin kotu ya haifar da rudani" - Effiong

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ba ta da wata rawar da za ta iyaa takawa, kuma ba za ta iya yin katsalandan a harkokin sarauta.

Barista Effiong ya ce:

“Batun da ya shafi masarautu na karkashin ikon jiha ne, gwamnatin tarayya ba ta da wata rawar da ta za ta iya takawa a irin wannan rigimar.
"Yana a karkashin hurumin kotun jihar sauraron shari'ar da ta shafi sarauta. Akwai rudani a hukuncin da Mai shari’a Liman na kotun tarayya da ke Kano ya yanke

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamna Abba na cikin Matsala, an bayyana sahihin Sarkin Kano

"Yadda za a kawo ƙarshen rigimar" - Effiong

Barista Effiong ya ce Gwamna Abba Yusuf na da hurumin ya rusa masarautar Kano gaba dayanta, wanda zai kawo karshen rikicin sarautar.

A cewar lauyan, babu abin da zai faru wai don Gwamna Yusuf ya rusa masarautar, domin ba kundin tsarin mulkin kasa ne ya samar da ita ba.

"Ko yau gwamnatin jihar Kano da majalisar jihar suka yi niyya za su iya rusa masarautar Kano, kuma ba abin da zai faru."

Sanusi II ya yi magana kan tsige shi a 2020

A wani labarin, mun ruwaito cewa Muhammadu Sanusi II ya bayyana dalilin da ya sa bai yi karar Abdullahi Ganduje ba a lokacin da aka fara tsige shi daga sarkin Kano a 2020.

Sanusi II ya bayyana cewa ko da a ce ya je kotu kuma kotu ta mayar da shi, ba zai iya yin aiki da gwamnatin Gwamna Ganduje ba tunda gwamnan ya nuna masa tsana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.