"Abin da Ya Tada Hankalin Abba Gida Gida Bayan Shiga Ofis" Inji Hadimin Gwamna

"Abin da Ya Tada Hankalin Abba Gida Gida Bayan Shiga Ofis" Inji Hadimin Gwamna

  • Abba Kabir Yusuf ya yi kokarin bunkasa ilmi a lokacin da yake kokarin zama gwamnan jihar Kano a zaben 2023
  • Shekara guda bayan shiga ofis, Mai girma gwamnan ya ayyana dokar ta-baci domin ganin an farfado da kimar ilmi
  • Hassan Sani Tukur a matsayinsa na mai ba gwamna Abba shawara, ya ce abin ya sukurkuce fiye da yadda ake tunani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A karshen watan Mayun 2023, Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan jihar Kano bayan ya lashe zabe a inuwar jam’iyyar NNPP.

Bayan watanni ana shari’a, Abba Kabir Yusuf ya gyara zama da kyau a kan kujerar mulki, ya gaji Dr. Abdullahi Umar Ganduje na APC.

Gwamna Abba Kabir
Gwamnan Kano ya koka kan yadda ilmi ya tabarbare a jihar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hirar Legit da Hadimin gwamna Abba

Kara karanta wannan

'Aminu Ado Bayero a makabarta yake zaune ba fadar Sarki ba' Inji Gwamnatin Abba

A wata zantawa da Hassan Sani Tukur, ya yi mana bayanin halin da Abba Kabir Yusuf ya samu gwamnatin Kano bayan APC ta bar mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Hassan Tukur yana cikin manyan masu taimakawa gwamnan Kano wajen harkokin sadarwa a kafafen sada zumunta na zamani.

Halin ilmin Kano ya girgiza Abba

Sannan ya ce gwamnatin Ganduje ba ta ba ilmi kason kirki a kasafin kudi ba, ganin yadda makarantu suka lalace ya tada hankalin gwamna.

Hadimin gwamnan ya ce lokacin da mai gidansa ya zama gwamna, sun samu abubuwa sun tabarbare fiye da yadda suka yi tunani a baya.

Ganin haka ne gwamnan jihar Kano ya sa dokar ta-baci na musamman a kan sha’anin ilmi.

"Abin ya wuce tunanin Abba Gida Gida"

"Bayan kafa gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf, tare da abubuwan da muka san game da gwamnatin baya,"

Kara karanta wannan

"Yadda Abba yayi abin da ba a taba gani ba a tarihin jihar Kano" Inji Hadimin Gwamna

"da mu ka shigo sai mu ka ga tabarbarewar ta wuce haka, abin da mu ka gani ya nunka abin da ake tunani."
"Mun zo mun iske tabarbarewa a duk abubuwan da ke taimakawa karantarwa; wurin karatu, kayan aiki da malamai."
"An samu lalacewar al’amura, mun tarar da makarantu bila-adadin babu wurin zaman yara, ana karatu a kasa."
Mun iske ban-dakuna sun lalace a wasu makarantu har ta kai an rufe su, an bar abubuwa ana kallonsu a haka."

- Hassan Sani Tukur

Yadda Abba ya samu malamai da makarantu

A hirarmu da mai ba gwamnan shawara, ya ce gwamnatinsu ta NNPP ta ci karo da karancin kayan aiki a makarantun da ke jihar Kano.

Baya ga haka, Hassan Tukur ya ce babu tsarin da aka tanada domin walwalar malamai baya ga karancin kwararru da ake fama da su.

Atiku yana goyon bayan Ganduje

A baya an kawo rahoto cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya samu goyon baya a kan masu harin kujerarsa a jam’iyyar APC mai mulki.

Atiku Abubakar Isah bai ganin Yahaya Bello zai iya karbar NWC daga hannun tsohon gwamnan Kano, ya ce bai dace a canza Ganduje ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng