Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Neman Fatattakar Shugaban EFCC Daga Mukaminsa

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Neman Fatattakar Shugaban EFCC Daga Mukaminsa

  • Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da korafin neman sallamar shugaban EFCC, Ola Olukoyede daga mukaminsa
  • Wani lauya mai suna Victor Opatola shi ya ke kalubalantar nada Olukoyede a matsayin shugaban hukumar
  • Opatola ya ce Olukoyede ba shi da kwarewa na tsawon shekarun da ya kamata ya kasance shugaban hukumar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin neman korar shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede.

Kotun ta yi fatali da neman sallamar Olukoyede bayan wani lauya, Victor Opatola ya kalubalnci Bola Tinubu kan nadin shugaban hukumar.

Kotu ta yi hukunci kan neman korar shugaban EFCC
Kotun Tarayya ta yi watsi da korafin da ke neman a sallami shugaban EFCC, Ola Olukoyede. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: UGC

Lauya ya kalubalanci nadin Olukoyede a EFCC

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Alkalin kotun, Mai Shari'a, Obiora Egwuatu shi ya dauki wannan mataki inda ya ce korafin ya rasa hujjoji a shari'ance, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan da ke kalubalantar nadin Olukoyede ya ce shugaban hukumar ba shi da kwarewa na shekarun da ake bukata wajen rike EFCC.

EFCC: An kai majalisa da minista kotu

Daga cikin wadanda ake karar akwai shugaban kasa da Majalisar Tarayya da Ministan Shari'a da kuma Ola Olukoyede, Vanguard ta tattaro.

Har ila yau, wadanda ake karar sun bukaci kotun ta yi watsi da korafin lauyan saboda rashin hujjoji ingantattu.

Lauyan EFCC ya kalubanci korafin Opatola

Lauyan shugaban EFCC, Olumide Fusika ya kalubalanci korafin inda ya kare Ola Olukoyede kan nadinsa.

Fusika ya ce Olukoyede ya cancanci nadin bayan rike mukamin sakataren hukumar da kuma zuwa matakin aiki na 17.

Kara karanta wannan

Sarkin da ya fi daɗewa a sarauta a Arewa ya rasu, Bola Tinubu ya tura saƙon ta'aziyya

Bayan sauraran duka bangarorin biyu, Mai Shari'a Egwuatu ya daga sauraran karar zuwa yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.

Bayan tuhumar EFCC, Yahaya Bello ya saduda

A wani labarin, kun ji cewa ana sa ran tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai gurfana a gaban kotu a gobe Alhamis 13 ga watan Yunin 2024.

Bello zai kawo kansa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bayan wasan tsere da hukumar EFCC kan zargin badakalar kuɗi har N80bn.

Lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed ya ce Bello ba ya tsoron EFCC amma yana tsoron halin da rayuwarsa za ta kasance a hannunsu a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.