Sarautar Kano: Abba Hikima Ya Magantu Kan Sahihin Sarkin Kano, Ya Jero Dalilai

Sarautar Kano: Abba Hikima Ya Magantu Kan Sahihin Sarkin Kano, Ya Jero Dalilai

  • Fitaccen lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya bayyana matsayar hukuncin sarautar da aka yanke a jiya Alhamis
  • Abba ya ce a mahangar shari'a, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ne sahihin sarki kamar yadda doka ta tabbatar
  • Wannan martani na Hikima na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci a jiya Alhamis 20 ga watan Yunin 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya yi martani kan dambarwar sarautar jihar Kano.

Abba ya ce babu wani rudani kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya inda ya ce komai a bayyane yake.

Abba Hikima ya fadi sahihin Sarkin Kano a yanzu
Fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin Sarki. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Hikima, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Abba Hikima ya fadi sahihin sarki

Kara karanta wannan

Lauya ya ci gyaran gwamna, ya fassara hukuncin Alkali a shari’ar masarautar Kano

Hikima wanda dan asalin jihar Kano ne ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya ce a yanzu sahihin Sarkin Kano a mahangar doka shi ne Aminu Ado Bayero saboda kotu ta yi fatali da matakan Gwamna Abba Kabir.

Ya ce kafin wannan lokaci kotun ta ba da umarni kan matakin da gwamnan ya dauka bayan mayar da Muhammadu Sanusi II.

"Kotu ta fadi wanene Sarkin Kano" - Lauya

"Ba daidai ba ne a ce akwai rikitarwa kan lamarin, hukuncin a bayyana yake saboda umarnin farko ya nuna duka umarnin da Abba ya dauka kan masarautun an jingine su gefe."
"Ya kamata mu fadawa mutane ba wani matsala a hukuncin saboda tun farko 23 ga watan Mayu kotu ta umarci duka wadanda suke cikin shari'ar da su koma baya kafin rushe masarautun kafin sanya hannu a dokar."

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauyoyin Arewa sun yabawa hukuncin kotu, sun gargaɗi gwamna Abba

"A maganhar shari'a Sarkin Kano shi ne Aminu Ado Bayero saboda kotun ta rusa matakan da aka dauka na mayar da Sanusi II."

- Abba Hikima

Kano: Lauyoyin Arewa sun yabawa hukuncin kotu

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Lauyoyi da ke Arewacin Najeriya (NCNLPIA) ta yi martani kan hukuncin kotu game da masarautun jihar Kano.

Kungiyar ta yabawa hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta mayar da Aminu Ado Bayero kan kujerar sarauta.

Shugaban kungiyar, Napoleon Otache shi ya bayyana haka ranar Juma'a 21 ga watan Yunin 2024 a bayan yanke hukuncin kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel