Rigima Ta Kaure Tsakanin ’Yan Bindiga, Su Na Ta Kashe Junansu da Kansu a Jejin Zamfara
- Tawagar 'yan bindiga biyu ma su hamayya da juna sun kaure da faɗa tsakaninsu kan yunkurin kwace ikon wani yankin Zamfara
- Lamarin ya faru ne a wani jejin karamar hukumar Maru, jihar Zamfara inda ‘yan ta’addan suka yi kaurin suna wajen farmakar jama'a
- Majiyoyin leken asiri sun shaida cewa akalla ‘yan ta’adda 16 suka mutu a arangamar, ciki har da wasu manyan jagorori guda biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Maru, jihar Zamfara - A wani lamari mai ban mamaki, wasu gungun 'yan bindiga sun kashe junansu a wani kazamin fada da ya kaure tsakanin bangarorin da ke gaba da juna.
Lamarin ya faru ne a wani jejin karamar hukumar Maru, jihar Zamfara inda ‘yan ta’addan suka yi kaurin suna wajen hana jama'a zaman lafiya.
A cewar rahoton da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X, fadan ya barke ne a lokacin da wani bangare ya yi yunkurin kwace wani yanki da ke hannun dayan bangaren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga 16 sun mutu yayin artabu
An gwabza kazamin fada, inda majiyoyin leken asiri suka shaidawa Zagazola Makama cewa an kashe ‘yan ta’adda akalla 16 a arangamar.
Daga cikin manyan kwamandojin ‘yan fashi da aka halaka a wannan fadan, akwai Alhaji Nagala da Maikube, wadanda suka yi kaurin suna a ta'addanci.
Majiyoyin sun ce an shafe watanni ana takun saka tsakanin bangarorin da ke gaba da juna, inda a makwannin baya-bayan nan rikici ya yi tsamari.
Hukumomi sun yi maraba da fadan
Ana dai kallon wannan arangama a matsayin wani gagarumin koma baya ga kungiyoyin ta'addancin, wadanda suka samu tarwatse sakamakon rarrabuwar kawuna.
Hukumomin kasar dai sun yi na'am da wannan labari, inda suka bayyana cewa mutuwar 'yan ta'adda wani ci gaba ne mai kyau a fagen yaki da ta'addanci.
Wannan lamarin dai yana nuni da cewa babu amana tsakanin ‘yan ta’adda, za su iya juya wa juna baya, kuma dama akidarsu ta samo asali ne da tashin hankali da barna.
An kama masu garkuwa da mutane
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin sun kware wajen yin garkuwa da mutane a yankunan jihar Taraba.
Jami'an soji da ke a bataliya ta 6 ne suka kama mutanen bayan shafe watanni suna bibiyarsu, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin tare da bayar da karin bayanan sirri.
Asali: Legit.ng