Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Faɗi Matakin da Ya Ɗauka Kan Hukuncin Soke Naɗin Sanusi II

Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Faɗi Matakin da Ya Ɗauka Kan Hukuncin Soke Naɗin Sanusi II

  • Gwamnatin Kano karƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin soke naɗin Muhammadu Sanusi II
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Alhaji Baba Ɗantiye ne ya tabbatar da haka a wani saƙo da ya turawa manema labarai
  • A jiya Alhamis ne babbar kotun tarayya ta rusa duka matakan da Abba ya ɗauka yayin zartar da sabuwar dokar masarautar Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

Kotun ta soke matakan da Gwamna Abba Kabir Yusuf a ɗauka na mayar da Sanusi II kan karagar mulki saboda ƙin bin umarninta a lokacin.

Kara karanta wannan

"Yana da ɗaure kai," Falana ya faɗi kuskuren da aka yi a hukuncin shari'ar sarautar Kano

Gwamna Abba tare da Sanusi II.
Gwamnatin jihar Kano ta ce z ata ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Wane mataki Gwamna Abba ya ɗauka?

A halin yanzu gwamnatin Kano ta sha alwashin ɗaukaka ƙara kan wannan hukuncin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan yada labarai, Baba Dantiye, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta daukaka kara kan hukuncin.

"Eh, za mu daukaka kara," in ji shi a cikin sakon da ya aike wa daya daga cikin wakilan jaridar yayin da yake amsa wata tambaya.

Hukuncin da kotu ta yanke a Kano

Idan ba ku manta ba Alkali Abdullahi Liman ya yanke hukuncin jingine matakin Gwamna Abba na mayar da Sanusi II kan sarauta saboda ya saɓawa umarninsa.

Sai dai ya ce hakan bai shafi sabuwar dokar masarautar Kano ta 2024 ba amma ya soke abubuwan da suka biyo baya kamar zartar da dokar da kuma naɗin Sanusi II.

Kara karanta wannan

Kano: Bidiyon buldoza ya ja hankalin mutane yayin da Abba ke shirin rusa Fadar Aminu

“Na saurari faifan sautin gwamnan a cikin harshen Hausa da Ingilishi bayan ya rattaɓa hannu a kan dokar, kuma na gamsu cewa wadanda ake kara ba su da masaniya game da umarnin.
"Bisa gamsuwa da cewa waɗanda ake kara ba su samu umarnin kotun a kan kari ba, kotu ta soke matakin saboda ya saɓawa umarnin da ta bayar na dakatar da naɗin Sanusi II."

- In ji mai shari'a Liman.

Alkalin ya ƙara da cewa tun farko idan da waɗanda ake ƙara sun bi umarnin kotu da hakan ba ta faru ba, kuma za a basu damar aiwatar da manufarsu, Premium Times ta ruwaito.

Gwamnatin Abba za ta gyara fadar Nassarawa

A wani rahoton kun ji rikicin sarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ya ɗauki sabon salo yayin da aka fara shirin rusa ƙaramar fada

Wani bidiyo da ya bazu a soshiyal midiya ya nuna yadda gwamnatin Kano ta tura motocin Buldoza zuwa fadar da Aminu ke ciki, mutane sun yi martani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262