Sojoji Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane da Suka addabi Taraba, Sun Ba da Bayanai

Sojoji Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane da Suka addabi Taraba, Sun Ba da Bayanai

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a garuruwan jihar Taraba
  • Jami'an soji da ke a bataliya ta 6 ne suka kama mutanen bayan shafe watanni suna bibiyarsu domin tattara rahotanni
  • Wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun mallaki bindigogi kirar Ak47 kuma sansaninsu yana Gadawa a kauyen Zunguri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Taraba - A wani gagarumin ci gaba da aka samu, dakarun bataliya ta shida ta sojojin Najeriya sun kama wasu riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane biyu da suka addabi jihar Taraba.

An ruwaito cewa, an kama wadanda ake zargin, Fankau Algaji Laulo da Ahmadu Buba Ango a wani samamen rundunar hadin guiwa ta sojoji da mafarauta.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da wani soja ya hallaka farar hula a Abuja

An kama masu garkuwa da mutane a Taraba
Sojoji sun kama mutane 2 da ake zargi da garkuwa da mutane. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An kama masu garkuwa da mutane

Mai a sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, wanda ya wallafa labarin a shafinsa na intanet ya ce an kama mutane ne a Garin Baka da Gongon Maliki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar mai tushe ta bayyana cewa, jami'an tsaro sun shafe watanni suna sa ido kan mutanen biyu bayan rahoton su da aka kai kan zargin suna satar mutane a yankin.

Wadanda ake zargin sun yi jawabi

A halin yanzu dai ana ci gaba da yiwa wadanda ake zargin tambayoyi, kuma bincike na farko ya nuna cewa suna da hannu wajen yin garkuwa da mutane da dama.

Wadanda ake zargin sun kuma bayyana cewa sun mallaki bindigogi kirar Ak47 kuma sansaninsu yana Gadawa a kauyen Zunguri a karamar hukumar Baisa I Kurmi.

Sun kuma kara da cewa 'yan tawagarsu ta garkuwa da mutane sun fito ne daga jihohin Adamawa, Gombe, Filato da kasar Kamaru.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, miyagu sun yi ta'asa har da jikkata yan sanda

Majiyar sojojin ta bayyana cewa kama wadannan mashahuran masu garkuwa da mutanen biyu zai kawo karshen satar mutane a yankin da tabbatar da tsaron al’umma.

Najeriya za ta sayo jiragen yaki 50

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar sayo jiragen sama na yaki 50 domin karfafawa sojojin saman kasar guiwar yaki da 'yan ta'adda.

An ruwaito cewa za a yi amfani da jiragen wajen karfafa kai hare-hare kan 'yan ta'addan da suka addabi jihohin Arewa maso Yamma da tsakiyar kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel