'Yan Bindiga Sun Mamaye Dajin Kainji, Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Mataki

'Yan Bindiga Sun Mamaye Dajin Kainji, Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Mataki

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta ce za ta mallaki sababbin jiragen sama guda 50 domin karfafa yaki da ‘yan ta’adda a fadin kasar
  • Hafsan sojin saman Najeriya, Marshal Hassan Bala Abubakar ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da wasu ayyuka a Katsina
  • Za a yi amfani da jiragen wajen karfafa kai hare-hare kan 'yan ta'addan da suka addabi jihohin Arewa maso Yamma da tsakiyar kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Katsina - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na karfafa ayyukan ta na yaki da ‘yan ta'adda ta hanyar sayo sababbin jiragen sama na yaki guda 50.

Shirin dai na da nufin karfafa ayyukan tsaro a yankin Arewa maso Yamma da kuma fadin Najeriya yayin da ‘yan ta’adda suka mamaye dajin Kainji a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane da suka addabi Taraba, sun ba da bayanai

Gwamnatin Najeriya za ta sayo jiragen yaki guda 50
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce za ta mallaki sababbin jiragen sama guda 50. Hoto: @officialABAT, @NigAirForce
Asali: Facebook

Hafsun sojin sama, Marshal Bala Abubakar ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da sababbin kayayyakin aiki a sansanin FOB 213 da ke jihar Katsina, in ji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta sayo jiragen yaki

Hafsan hafsan sojin saman ya bayyana cewa, jiragen za su hada da jiragen yaki masu saukar ungulu kirar AH-1 guda 12, da jiragen kai hari na M-346 guda 24.

Sauran da jirage masu saukar angulu kirar Augusta Westland 109 guda 12, da kuma jiragen daukar sojoji da kaya kirar Casa 295 guda biyu.

Kafar labaran VOA ta ruwaito Marshal Bala Abubakar ya ce ana sa ran Najeriya za ta karbi jiragen guda 50 daga yanzu zuwa shekara ta gaba.

Mike Ejiofor ya soki kudirin sayo jiragen

Sai dai wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Mike Ejiofor ya ce sayo jiragen sama 50 abu ne da ya wuce gona da iri kuma saka kudi a inda bai dace ba.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga sama da 100 ana shagalin Sallah a Arewa

Mike Ejiofor ya ce:

"Na san hakan zai karfafa yaki da ta'addanci, amma na yi imanin cewa ya kamata mu maida hankali kan kasa fiye da iska. Ba mu fuskantar baranazar yaki a yanzu."

Ya ce kamata a yi amfani da kudin wajen horar da sojoji da kuma samar da walwala ga sojojin kasa, wadanda su ne suka fi yin arangama da 'yan ta'addan.

'Yan bindiga sun farmaki sakatariyoyin Anambra

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun farmaki sakatariyar karamar hukumar Ogbaru da ke a jihar Anambra.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da rahoton kai farmakin, inda ya ce babu asarar rayuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel