Sarautar Kano: Yaron Sanusi II Ya Yi Martani Bayan Hukuncin Kotu Kan Dokar Masarauta

Sarautar Kano: Yaron Sanusi II Ya Yi Martani Bayan Hukuncin Kotu Kan Dokar Masarauta

  • An fara zaman dari-dari a birnin Kano biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke kan dokar da rusa masarautun jihar guda biyar
  • A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya ta yi watsi da matakan da Gwamna Yusuf ya dauka na tsige Aminu Ado Bayero
  • Sai dai Ashraf Sanusi, dan Sarki Muhammadu Sanusi II, ya mayar da martani game da soke nadin mahaifinsa da kotun ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Ashraf Sanusi, dan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi martani yayin da wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta soke nadin mahaifinsa.

A ranar Alhamis ne kotun a karkashin Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta soke duk wasu matakai da aka dauka wajen dawo da Sanusi II kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Hukuncin masarautar Kano ya lasawa bangarorin da ke rikici zuma a baki

Rikicin masarautar Kano: Dan Sanusi II ya mayar da martani kan hukuncin da kotu ta yanke
Ashraf Sanusi tare da mahaifinsa, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Hoto: @Adam_L_Sanusi
Asali: Twitter

'Dan Sanusi II ya magantu hukuncin kotu

Sai dai a bayan kotun ta yanke wannan hukuncin, sai yariman na Kano ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, yana mai godiya ga Allah ga wannan hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ashraf ya yi addu'ar Allah ya kare kowa daga makiya da masu hassada, ya wallafa sakon ne tare da hotunan mahaifinsa, Sanusi II da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Dan Sanusi, ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Alhamdulillah. Allah ya karemu daga girman kai, hassada, da kyamar mutane, da kuma nuna munanan dabi'u walau a furucin baki ko a aikace."

'Yan Najeriya sun caccaki dan Sanusi

'Yan Najeriya sun shiga sashen sharhi tare da mayar da martani ga sakon da dan Sanusi ya wallafa.

@Abdulrahman0gml:

"Allah ka bamu 'ya'ya salihai wadanda zasu kawo alkairi ga al'ummah."

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku fahimta a hukuncin soke naɗin Sanusi II

@mujahid00033:

"Wane ne sarki a yanzu? Al'aminun ne ko mai martaba?"

@abdulla14305642

"Alhamdulillah. Kotu ta ladabtar da ku."

@TahirSuleimanM1:

"Idan suka ka farmaki mahaifinka ka kira shi da hassada amma idan aka farmaki Aminu Ado ka kira shi da me?"

"Har yanzu Sanusi II ne sarki" - Daderi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta dage kan cewa Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano duk da babbar kotun tarayya ta rusa batun nadin da aka yi masa.

Kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.