Babbar Kotun Tarayya ta yi Hukunci kan Dambarwar Masarautar Kano

Babbar Kotun Tarayya ta yi Hukunci kan Dambarwar Masarautar Kano

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano tun bayan rushe masarautun jihar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi
  • Mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman a hukuncin da ya zartar a yau ya kama gwamnatin Kano da bijirewa umarnin kotu wajen maido Muhammadu Sanusi II
  • Wannan bai nufin Aminu Ado Bayero ya dawo karaga, Kotu ta tabbatar da ingancin dokar da 'yan majalisar dokoki su ka kawo wanda gwamna ya rattabawa hannu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta duba dokar da majalisar dokokin Kano ta yi amfani da ita wajen nada sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Kotu ta soke nadin da aka yiwa Sanusi II? Ga karin haske kan hukuncin

Kotun tarayyar ta zartar da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ki bin umarnin ta wajen aiwatar da sabuwar dokar masarautu.

Masarauta
Kotu ta yanke hukunci kan sarautar Kano Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Kotu ta yi hukunci a shari'ar sarautar Kano

Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf da majalisar dokokin jihar ta mayar da sarki Sanusi II kujerarsa tare da sauke sarakunan da Ganduje a nada a shekarar 2020.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta ce an yi hakan ne duk da akwai umarnin da aka ba da cewa a dakata da maganar rusa masarautu da nada sabon sarki a Kano.

Basaraken Kano ya shigar da kara kotu

Tun bayan tunbuke sarki Aminu Ado Bayero na Kano, da sauran sarakunan Kano, basarake kuma daya daga masu nada sarki Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da kara kotu, Justice watch News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi magana yayin da ake jiran yanke Hukunci kan sahihancin tuɓe Sarkin Kano

Dan Agundi yana karar gwamnatin Kano na rushe masarautar Kano wanda ya ce an keta masa ‘yancinsa na dan Adam, kamar yadda lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN) ya shaidawa kotun.

Hukunci kan shari'ar masarautar Kano

A hukuncin da ya yanke a yau, mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya ki amincewa ya haramta dokar masarautar Kano.

Alkali Liman ya yarda cewa an tsige Aminu Bayero da sauran sarakuna, sai dai ya ce an yi masa rashin kunya wajen kin bin umarni.

Daily Nigerian ta ce za a garzaya zuwa kotun daukaka kara domin a karasa shari'ar.

Kotu ta magantu kan shari'ar masarauta

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman ta magantu kan sahihancin dokar rushe masarautu,

Magatakardar kotun ya shaidawa lauyoyin bangarorin biyu cewa mai shari'a Muhammad Abdullahi Liman ya dage zaman kotun zuwa karfe 2:00 na rana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.