Asirin Ma'aikatan Bogi ya Tonu, Wasu Suna Cin Albashi Duk da Sun Bar Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta bankado wasu ma’aikata da su ka ajiye aiki kuma su ka tsallaka kasashen ketare amma ana ci gaba da biyansu albashi bayan tafiya ba bisa ka'ida
- Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr. Folasade Yemi Esan ce ta bayyana haka a a ranar Laraba, inda ta ce an gano ma’aikatan ne bayan gudanar da bincike da bukatar ma'aikatan su zo da kansu
- Dr. Esan ta bayyana cewa sun tantance ma’aikatan kasar nan da ake biya ta tsarin IPPIS, kuma an gano masu karbar albashin sun fi yawa a hukumomi maimakon ma'aikatu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta yi nasarar gano ma’aikatan bogi da ke zaune a kasashen ketare amma suna karbar albashi daga gwamnatin Najeriya.
Shugabar ma’aikatan ta kasa, Dr. Folasade Yemi Esan ce ta bayyana cewa an gano ma’aikatan ne bayan binciken tsarin biyan albashi na IPPIS a kwanan nan.
Vanguard News ta wallafa cewa Dr. Yemi Esan ta bayyana muhimmin aikin da ofishinta ya yi yayin bikin makon ma’aikata da ya gudana a Abuja ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma’aikatan bogi sun ajiye aiki
Shugabar ma’aikatan Najeriya, Dr. Folashade Yemi Esan ta bayyana cewa ma’aikatan bogi da gwamnati ta gano sun ajiye aiki, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.
Ta ce lamarin ya biyo bayan gano ma’aikatan da ke karbar albashi ba tare da sun yi aiki ba bayan tantancesu a ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Dr. Esan ta bayyana cewa gwamnati ta yi binciken ne saboda dakatar da albashin wadanda su ka bar aiki ba tare da bin ka’idoji ba.
Ta ce wadanda su ka bar aiki tare da fita kasashen waje kuma ana ci gaba da biyansu sun fi yawa a hukumomin gwamnati idan aka kwatanta da ma’aikatu.
Tsohon minista ya nemi kara albashin ma’aikata
A baya mun kawo labarin cewa tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Babatunde Raji Fashola ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu ta waiwayi albashin ma’aikatan kasar nan.
Fashola wanda tsohon gwamna ne a Legas na ganin kudin da ake biyan ma’aikatan ba zai ishe su gudanar da ayyukan yau da kullum ba, saboda haka ya nemi kara masu albashin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng