Yana kokarin Hana Fadan Daba, 'Yan Tauri Sun Kashe Shugaban Bijilanti a Kano

Yana kokarin Hana Fadan Daba, 'Yan Tauri Sun Kashe Shugaban Bijilanti a Kano

  • Kungiyar tsaron sa-kai ta bijilanti ta tsunduma cikin alhini a Kano bayan fadan daba tsakanin unguwanni biyu a karamar hukumar Gwale ya yi sanadiyyar kashe daya daga cikin shugabanninta
  • Kwamandan bijilanti a Gwale, Mukhtar Garba Baballiya ya rasu a harin da 'yan daba su ka kai Ja'en Unguwar Lalle a hanyarsa ta fitowa daga ofis jim kadan bayan dakile harin daba a yankin
  • Jami'in hulda da jama'a na kungiyar, Kamalu Adam Sudawa ya shaidawa Legit Hausa cewa su na kokari sosai wajen kare rayukan jama'a, amma su na bukatar taimakon jama'a sosai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar tsaron sa kai ta ‘yan bijilanti ta rasa daya daga shugabanninta a karamar hukumar Gwale yayin da ya ke kokarin hana fadan daba tsakanin ‘yan daba a unguwanni biyu da ke yankin.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Kwamandan kungiyar bijilanti na Kano, Shehu Rabi’u ne ya tabbatarwa da Legit Hausa rasuwar Mukhtar Garba Baballiya a yammacin Laraba, wanda ke kokarin shiga tsakanin ‘yan daba.

Fadan Daba
Daya daga shugabannin bijilanti ya rasu a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rahotanni sun bayyana cewa fadan daba ya kaure tsakanin ‘yan daba da ke Ja’en makera da na Ja’en unguwar lalle, inda a nan ne aka yi masa saran da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mu na bukatar dauki,” Bijilantin Kano

Kungiyar bijilanti a Kano ta bayyana cewa ta na cikin alhinin rashin daya daga shugabannin bijilanti a karamar hukumar Gwale yayin harin daukar fansa da ‘yan daban Ja’en Makera su ka kai unguwar lalle.

Kakakin kungiyar, Kamalu Jibrin Adam Sudawa ya shaidawa Legit Hausa cewa jami’ansu sun dakile yunkurin fadan daba na farko, amma a na biyun ne aka sari kwamandan yankin .

Kara karanta wannan

PDP ta tsoma baki kan rikicin Ribas, yayin da APC ke neman a sanya dokar ta baci

Ya ce ‘yan daban sun sari marigayi Baballiya a kai da wasu bangarorin jikinsa, kuma a nan jini ya debe shi har aka rankaya da shi asibiti, amma rai ya yi halinsa.

Sudawa ya kara da neman tallafin jama’ar unguwannin Kano da bayanai domin sun san matasan da ke aikata danyen aikin, da kayan aiki da kuma addu’a.

'Yan sanda sun magantu

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da cewa fadan daba a karamar hukumar Gwale ya yi sanadiyyar kisan daya daga shugabannin bijilanti a yankin, solace base ta wallafa.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bayan harin ne aka akai Mukhtar Garba Baballiya asibitin kwararru na Murtala, kuma a nan aka tabbatar da rasuwarsa.

"Za a kawo Boko Haram Kano" - Kwankwaso

A wani labarin kun ji cewa jagaoran darikar kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin sanya dokar ta baci a Kano.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a Ado Bayero Mall a Kano, har yanzu ana kokarin kashe wutar

Sanata Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya da kokarin kawo matsalar tsaro Kano domin cimma bukatar kashin kai, amma ya ce mutanen Kano ba za su amince ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.