'Yan Bindiga Sun Hallaka Matashi Bayan Ya Kai Musu Kudin Fansar N16m a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Hallaka Matashi Bayan Ya Kai Musu Kudin Fansar N16m a Kaduna

  • An shiga jimami a ƙaramar hukumar Jere ta jihar Kaduna bayan ƴan bindiga sun hallaka wani matashi da ya kai musu kuɗaɗen fansa
  • Matashin wanda da shi aka yi ciniki kan kuɗin fansa da ƴan bindigan ya kai musu Naira miliyan 16 da babura uky domin su sako wasu mutane tara
  • Sai dai, bayan ya ba su kuɗaɗen da baburan, sun hallaka shi har lahira saboda abin da suka bayyana da cewa ya yi musu tsaurin ido lokacin ciniki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun harbe wani matashi ɗan shekara 27 mai suna Abba, bayan ya kai musu kuɗin fansa a jihar Kaduna.

Matashin ya kaiwa ƴan bindigan Naira miliyan 16 da babura uku domin sako wasu mutane tara da suka yi garkuwa da su a garin Jere da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki, 'yan bindiga sun hallaka Amarya mako 1 tak bayan ɗaura aurenta

'Yan bindiga sun hallaka matashi a Kaduna
'Yan bindiga sun hallaka mai kai kudin fansa a Kaduna
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ce ƴan bindigan sun mamaye wasu gidaje a Unguwar Iya da ke Jere a ranar 16 ga Afrilu, 2024, inda suka yi garkuwa da mutane tara tare da neman a ba su Naira miliyan 30.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka hallaka matashin

Wani mazaunin yankin, Shuaibu Hussaini, ya tabbatar da kashe Abba yayin da yake zantawa da wakilin jaridar ta wayar tarho a ranar Laraba.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar bayan matashin wanda da shi aka yi cinikin kuɗin fansan ya je kai Naira miliyan 16 da babura uku ga shugaban ƴan bindiga a wani wuri da ke yankin.

Ya ce shugaban ƴan bindigan bayan ya karɓi kuɗin fansa da baburan, sai ya ɗaure marigayin da igiya sannan ya buɗe masa wuta.

'Yan bindiga: Dalilin kashe mai kai kudin fansa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 6 yayin wani hari a Kaduna

"Ɗaya daga cikin mutanen da aka sako cikin waɗanda aka sace ne ya ce shugaban ƴan bindigan ya yi iƙirarin cewa sun kashe Abba ne saboda ya yi musu tsaurin ido yayin ciniki kan kuɗin fansan."
"Sai a lokacin da wani ɗan uwansa ya yi ƙoƙarin sanin inda Abba yake bayan ya kai kuɗin fansan, sannan shugaban ƴan bindigan ya ce su je wani waje su ɗauko gawarsa."

- Shuaibu Hussaini

Ƴan sanda ba su san da ta'adin ƴan bindigan ba

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, bai ce komai ba kan lamarin.

Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakinsa kan lamarin, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar mutum shida yayin da wasu da dama kuma aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ido na ganin ido, sun kashe bayin Allah ranar yawon Sallah

Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin Bauda da Chibiya a gundumar Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel