Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya Saduda, Ya Nemi Ayi Sulhu da Gwamnati

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya Saduda, Ya Nemi Ayi Sulhu da Gwamnati

  • Lauyoyin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar ballewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu sun ce wanda su ke wakilta ya shirya hawa teburin tattaunawa
  • Jagoran lauyoyin Mista Alloy Ejimakor ne ya shaidawa kotu haka a zamansu na yau Laraba saboda fargabar kin amincewa da bukatunsu da kotu za ta iya yi
  • Daga cikin bukatun akwai mika shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) gidan yari saboda bijirewa umarnin kotu, da kuma tuhumar hurumin kotun kanta kan shari'ar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja - Bayan shafe shekaru a tsare, shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya zubar da makaman yaki inda ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tattauna da wakilan gwamnati.

Kara karanta wannan

PDP ta tsoma baki kan rikicin Ribas, yayin da APC ke neman a sanya dokar ta baci

Nnamdi Kanu ya shaidawa kotun tarayya da ke zamanta a Abuja cewa ya shirya zaman yayin da aka ci gaba da shari’ar tuhume-tuhume kan ta’addanci da cin amanar kasa da ake yi masa.

Nnamdi
Jagoran IPOB ya nemi zama da gwamnati Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Vanguard News ta tattaro lauyoyin Mista Kanu ne su ka bayyana matsayarsu karkashin jagoranicn Mista Alloy Ejimakor, inda ya ce sashe na 17 na dokar babbar kotun tarayya ya bayar da damar cimma masalaha ta tattaunawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin lauyoyin Nnamdi Kanu na neman sulhu

Jagoran lauyoyin Nnamdi Kanu, Alloy Ejimakor, ya shaidawa kotu cewa sun nemi amfani da sashe na 17 na dokar babbar kotun tarayya ne domin fargabar za ta soke bukatunsu guda biyu.

Bukatarsu ta farko ita ce kotu ta garkame shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi bisa zargin karya umarnin kotu, kamar yadda TVC News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a Ado Bayero Mall a Kano, har yanzu ana kokarin kashe wutar

Sai bukatarsu ta biyu ta tuhumar kotun da cewa ba ta da hurumin sauraron shari’ar, kuma tuni lauyan gwamnati Adegboyega Awomolo ya yi martani.

Ya ce babban lauyan kasa ne kawai ya ke da ikon tattunawa kan zarge-zargen da su ka shafi cin amanar kasa da ta’addanci.

Kotu ta hana Nnamdi Kanu beli

A baya mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu bayan lauyoyinsa sun bukaci haka.

Mai shari'a Binta Nyako ta kuma yi umarnin gaggauta ci gaba da shari'ar da ake yi tsakanin gwamnatin Najeriya da Mista Kanu kan zargin ta'addanci da cin amanar kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel