Hukumar PSC Ta Buƙaci Tinubu Ya Kori Sufeton ’Yan Sanda, Ta Bayyana Dalili
- A makon da ya wuce sufeton 'yan sanda na kasa IGP Kayode Egbetokun ya ce akwai badakala cikin daukan sababbin yan sanda da aka yi
- Biyo bayan kalamansa, hukumar yan sanda ta kasa (PSC) ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kori babban jami'in tsaro
- Har ila yau, hukumar PSC ta bayyana dalilan da suka sa ta buƙaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kori IGP Kayode Egbetokun cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - An samu takun saƙa tsakanin rundunar ƴan sanda ta kasa da hukumar 'yan sandan Najeriya (PSC).
Rikicin ya samo asali ne daga fatalin da rundunar yan sanda ta yi da sunayen wadanda aka ce sun yi nasarar samun aiki a bana.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hukumar kula da aikin 'yan sanda (PSC) ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya kori sufeton 'yan sanda kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar PSC ta bukaci korar IGP Kayode
Hukumar ta PSC ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya kori sufeton 'yan sanda, Kayode Egbetokun bisa shiga lamarin da bai shafesa ba.
PSC ta ce tantance jami'an yan sanda bai shafi rundunar 'yan sanda ba saboda haka bai kamata ta saka baki kan lamarin ba.
PSC ta zargi yan sanda da maguɗi
Hukumar PSC ta ce wasu jami'an yan sanda sun nufi saka sunayen bogi a yayin tantancewa amma basu samu dama ba.
PSC ta kara da cewa rundunar ba ta shirya bada horo ga sababbin yan sandan da aka dauka bane shi yasa take kawo korafi, rahoton Channels Television.
Jami'an PSC sun gudanar da zanga-zanga da wakoki a lokacin da suka mika korafin neman korar IGP Kayode Egbetokun.
Hakan kuma na zuwa ne bayan PSC a sake sunayen mutane 10,000 da suka samu nasarar shiga aikin dan sanda amma IGP Kayode ya ce an samu cin hanci wajen tantance mutanen.
An kashe 'yan fashi a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja tace an fafata tsakanin jami'an tsaro da 'yan fashi a karamar hukumar Abaji.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh ya ce an yi nasarar kashe 'yan fashi biyu a yayin fafatawar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng