"Ya Kamata Gwamnati ta Gyara Albashi, Farashi na Kara Hauhawa," Tsohon Ministan Buhari

"Ya Kamata Gwamnati ta Gyara Albashi, Farashi na Kara Hauhawa," Tsohon Ministan Buhari

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola (SAN) ya ga akwai dacewar gwamnati ta duba batun mafi karancin albashi saboda hauhawar farashi da ake fama da shi a Najeriya
  • Fashola, wanda tsohon minista ne a gwamnatin Muhammadu Buhari da ta shude na ganin ya kamata gwamnati ta biya ma'aikata abin da zai wadace su tusarrafin yau da gobe
  • Tsohon ministan ayyukan ya kuma ga rashin dacewar wani sashi na dokar mafi karancin albashi 2019 da ya ki tilastawa masu ma'aikata kasa da 25 biyan mafi karancin albashi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- Tsohon Ministan ayyuka, Babatunde Fashola ya ce ma’aikatan Najeriya na bukatar gwamnati ta biya su albashin da zai isa su gudanar da ayyukansu na yau da kullum duba da yadda ake samun hauhawar farashi.

Kara karanta wannan

'Kar ka fara da bada hakuri': 'Yan kasa sun yi martani ga Tinubu, sun fadi mafita ga Najeriya

Ya bayyana haka ne a cikin wata takarda da ya rubuta da ya yiwa lakabi da duba kan albashin ma’aikata, matsayata a kan batun.

Fashola
Tsohon Minista Fashola ya nemi karin albashin ma'aikata Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Tunde Fashola
Asali: Facebook

Tsohon Minista ya ce a kara albashi

Vanguard News ta wallafa cewa tsohon ministan ya ce hauhawar farashin kaya a kasar nan ya shafi kowa da kowa, saboda haka akwai bukatar gwamnati ta yi gyaran da zai cicciba halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunde Fashola ya ce akwai bukatar gwamnati ta yi duba na tsanaki kan albashin ma’aikata.

Doka ta sassauta biyan mafi karancin albashi

Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola ya ce akwai kuskure kan dokar da ta sassautawa wasu ma’aikatu da ke da ma’aikata kasa da 25 biyan mafi karancin albashi.

Channels Television ta wallafa tsohon shugaban na ganin sashe na 4(1)(b) na dokar mafi karancin albashi (2019) ya ce ba tilas ba ne ga wadanda ke da ma’aikata kasa da 25 su biya mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi biris da NLC, ta dage a kan biyan N62,000 ga ma'aikata

Ya na ganin irin wadannan kamfanoni na daukar ma’aikata da dama kuma marasa karfi daga cikin al’umma, saboda haka akwai alamar tambaya kan wa dokar ta ke karewa.

Matsayar tsohon gwamnan kuma babban lauya a kasar nan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun tsaiko kan batun mafi karancin albashi.

Majalisa za ta yi doka kan albashi

A baya mun kawo labarin cewa majalisar kasar nan ta bayyana shirinta na samar da dokar da za ta tilastawa gwamnoni biyan mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihohinsu.

Matakin na zuwa ne a lokacin da aka gaza samun matsaya kan batun mafi karancin albashin, kuma gwamnonin jihohi sun bayyana cewa ba za su iya biyan abin da NLC ta nema ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel