"So Kake Yi Tinubu Ya Mutu": Fadar Shugaban Kasa Ta Caccaki Peter Obi

"So Kake Yi Tinubu Ya Mutu": Fadar Shugaban Kasa Ta Caccaki Peter Obi

  • Fadar shugaban ƙasa ba ta ji daɗin kalaman da Peter Obi ya yi ba kan batun siyo sabon jirgin sama ga Shugaba Bola Tinubu
  • Bayo Onanuga ya caccaki ɗan takarar shugaban ƙasan a zaɓen 2023, inda ya tambaye shi ko yana son ya ga Tinubu ya mutu ne
  • Onanuga ya yi nuni da cewa siyo jirgin ya zama dole saboda wanda ake amfani da shi yanzu ya nuna alamar ya gaji da duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta caccaki Peter Obi kan kalaman da ya yi dangane da shirin siyan sabon jirgin sama ga Shugaba Bola Tinubu.

Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya caccaki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar Labour Party (LP) kan batun siyo jirgin saman.

Kara karanta wannan

"Ba ku kadai ba ne": Tinubu ya magantu kan talauci a kasa, ya kawo mafita

Bayo Onanuga ya caccaki Peter Obi
Fadar shugaban kasa ta yiwa Peter Obi martani kan siyo sabon jirgi ga Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Ana shirin siyawa Tinubu sabon jirgi

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin tsaro na ƙasa ya nemi gwamnatin tarayya ta siyo sababbin jiragen sama ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da yake martani dagane da hakan, Peter Obi, ya soki shawarar da kwamitin ya bayar.

A cewar Peter Obi, ko kaɗan shirin bai dace ba inda ya ƙara da cewa akwai buƙatar a riƙa mayar da hankali wajen jin daɗin ƴan ƙasa.

Wane martani aka yiwa Peter Obi?

Jaridar Vanguard ta ce da yake martani kan kalaman Peter Obi a wata hira da jaridar The Punch, Bayo Onanuga ya ce dole ce ta sanya ya kamata a siyo sabon jirgin.

Onanuga ya ce shirin siyo jirgin abu ne wanda kowace gwamnati mai hankali za ta yi saboda ba za ta yi wasa da lafiyar shugaban ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Dangote ya ziyarci Tinubu bayan an sauko Sallah, hotuna sun bayyana

"Shin Peter Obi yana son shugaban ƙasa ya mutu ne? Shin wannan ne fatan da yake yi?"
"Shin yana so ne ya ci gaba da tafiya a jirgi mara lafiya ya rasu kamar mataimakin shugaban ƙasar Malawi da shugaban ƙasar Iran? Ya zo ya gaya mana."
"Jirgin da yake amfani da shi a yanzu, an siyo shi ne lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo. Kusan shekara 20 kenan kuma ɗan ƙaramin jirgi ne."
"Jirgin ya samu matsala a lokacin da yaje Saudiyya. Sai da shugaban ƙasa ya shiga jirgin ƴan kasuwa domin zuwa UK. Ko masu kula da jirgin sun ce ya kamata a sauya shi."

- Bayo Onanuga

Peter Obi zai iya komawa PDP?

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa a 2023, Akin Osuntokun, ya yi magana kan yiwuwar ɗan takarar ya koma jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Akin Osuntokun ya bayyana cewa Peter Obi zai koma jam'iyyar PDP ne kawai idan za a ba shi tikitin yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel