1999 Zuwa 2007: Obasanjo Ya Tuno Halin da Ya Tsinci Najeriya Lokacin da Ya Karɓi Mulki

1999 Zuwa 2007: Obasanjo Ya Tuno Halin da Ya Tsinci Najeriya Lokacin da Ya Karɓi Mulki

  • Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya yi magana kan yadda ya gudanar da mulkin Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007
  • Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatinsa na daga cikin mafi nagarta wajen gudanar da mulki a tarihi, wadda ta taimakawa dimokuraɗiyya
  • Tsohon shugaban kasar ya ce ya samu Najeriya da tulin bashi, amma kafin ya sauka sai da ya tabbatar ƙasar ta samu rarar kudi a lalitarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abeokuta - Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa na daga cikin mafi nagarta wajen gudanar da mulki a tarihin Najeriya.

Olusegun Obasanjo ya koɗa gwamnatin tasa ne musamman kan abin da ya shafi tattalin arzikin ƙasar kafin ya hau mulki da kuma bayan ya sauka a 2007.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: An samu wani Alhaji 'dan Najeriya ya sake rasuwa a Saudiyya

Obasanjo ya yi magana kan nasarar mulkinsa
Obasanjo ya zayyana kokarin gwamnatinsa kan tattalin arziki. Hoto: @Oolusegun_obj
Asali: Getty Images

Jaridar The Guardian ta ruwaito Obasanjo ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya ke jawabi a wani taron matasan Safe Online da kamfanin NerdzFactory ya shirya a Abeokuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1999-2007: Nasarorin gwamnatin Obasanjo

Tsohon shugaban kasar ya tariyo irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu daga 1999 zuwa 2007 inda ya fara da batun biyan tulin bashin da ke wuyan Najeriya a lokacin.

Obasanjo ya ce:

"A lokacin da na karbi mulki, na gaji tulin basussuka, inda muke biyan $3.5bn duk shekara domin rage bashin. Ko da na sauka mulki, bashin da ake bin ƙasar bai wuce $36bn ba.
"Haka zalika, na bar akalla $50bn a lalitar gwamnati a lokacin da na bar mulki. Na kuma samar da rarar $25bn daga saida mai."

Tsohon shugaban kasar ya ce Najeriya ta iya yin shekaru 25 kan turbar dimokuraɗiyya ne sanadin kyakkyawan shugabancin da ya yi na shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta tanadi hukunci a shari'ar da Tinubu yake yi da Gwamnoni 36

Shawarar Obasanjo ga matasan Najeriya

Obasanjo ya gargadi matasa masu yiwa kasa hidima daga jihohin Legas da Ogun, wadanda suka halarci wannan taron da su sadaukar da rayuwarsu domin ci gaban kasa.

Tsohon shugaban kasar ya ce:

"Ci gaban kasa wani aiki ne na hadin gwiwa, kuma ilimi yana da matukar muhimmanci a matsayin wani kayan aiki da za ku iya amfani da shi wajen bayar da taku gudunmawar."

APC ta nemi a kama Sanata Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa Jam’iyyar APC ta nemi jami'an tsaro a Najeriya da su gaggauta cafke tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya nemi a tsare Kwankwaso har sai ya fadi sunayen wadanda ya ce suna daukar nauyin ta'addanci a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel