Gwamna Abba Ya Aika da Sako Ga Tinubu Ana Cikin Rikicin Sarautar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya aika da gaisuwar Sallah ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Sakon Gwamna Abba zuwa ga shugaban ƙasan ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rikicin sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero
- Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya ba manoman jihar damina mai albarka tare da jaddada ƙudirinsa na ba su taimakon da ya dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya aika da gaisuwar Sallah ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Saƙon na Gwamna Abba zuwa ga shugaban ƙasar ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rikicin sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Abba ya yi barka da Sallah ga Tinubu, Kwankwaso
Sanusi Bature, mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Yuni, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kuma aika da saƙon barka da Sallah ga jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, rahoton Pulse ya tabbatar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana muhimmancin lokacin bikin Sallah inda al'ummar Musulmi ke yin layya domin samun lada a wajen Allah.
"Ina amfani da wannan lokacin domin yin kira a gare mu da mu so juna tare da taimakon juna wanda hakan shi ne abin da lokacin Sallah yake koyarwa."
"Mu raba abin da Allah ya albarkace mu da shi da sauran ƴan uwanmu Musulmi maza da mata a faɗin jinar nan."
- Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba zai ba manoma tallafi
Daga nan sai gwamnan ya yi addu'ar samun damina mai albarka ta yadda manoman Kano za su samu yabanya mai yawa a daminar bana.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin ba manoma tallafin da ya dace ta hanyar ba su kayayyakin da suke buƙata.
Gwamna Abba ya gwangwaje maniyyatan Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake abin alheri ga maniyyatan jihar da ke ƙasar Saudiyya wajen gudanar da aikin Hajjin Bana.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gwangwaje mahajjatan da riyal 100 ga mahajjata 3,121 da suka fito daga fadin jihar baki daya.
Asali: Legit.ng