Kwastam Ta Gano Dabarar da Dillalai Suka Kirkiro Wajen Shigo da Haramtattun Kwayoyi

Kwastam Ta Gano Dabarar da Dillalai Suka Kirkiro Wajen Shigo da Haramtattun Kwayoyi

  • Hukumar kwastam ta koka kan yadda dilolin kwaya ke hada kai da jami'anta wajen samun hanyar safarar kayan maye cikin sauki
  • Shugaban hukumar ta kasa, Adewale Adeniyi ne bayyana haka yayin da yake baje kolin kayan shaye-shaye da suka yi nasarar kamawa
  • Adewale Adeniyi ya gargadi jami'an da suke aikata laifin da kuma bayyana irin matakin da hukumar ke shirin dauka a kansu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukumar kwastam ta Najeriya ta yi magana kan yadda bata gari ke hada kai da jami'anta.

Shugaban hukumar, Adewale Adeniyi ya ce masu safarar kwaya suna hada kai da jami'an kwastam domin kaucewa bincike.

Kara karanta wannan

Musulmi na murnar Sallah, mazauna Kano na bakin cikin kwace gonakinsu

Hukumar kwastam
Kwastam za ta hukunta jami'anta da suke taimakon dilolin kwaya. Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar ya yi gargadi mai zafi kan dukkan jami'in da aka kama da hannu cikin lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dilolin kwaya na kaucewa bincike

Shugaban hukumar kwastam ta kasa, Adewale Adeniyi ya ce a yanzu haka masu safarar kwaya sun fara hada kai da jami'ansu domin su rika samun tsira idan sun zo shingen bincike.

Adewale Adeniyi ya ce idan idan suka dauko haramtattun kwayoyi suna daukan jami'an kwastam ta inda da zarar an gansu ba za a binciki kayan da suka dauko ba.

An gano masu hada-kai da 'yan kwaya

Sai dai shugaban hukumar ya bayyana cewa a yanzu haka sun gano da yawa daga cikin wadanda ake hada baki dasu domin aikata laifin.

Adewale Adeniyi ya kuma tabbatar da cewa duk wanda dubunsa ya cika to lallai zai fuskanci fushin doka ba sani ba sabo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gano halin da miliyoyin dalibai ke ciki bayan an saida makarantu

Ya kuma kara da cewa hukumar ta riga ta gano wasu daga cikin masu laifin kuma tana daf da wallafa sunayensu da kuma kama su.

Shugaban ya fadi haka ne yayin baje-kolin miyagun kwayoyi da hukumar ta kama wanda kudinsu ya kai kimanin Naira biliyan 4.2.

Mahaifi ya kai dansa kotu

A Wani rahoton, kun ji cewa wani mahaifi da ya nemi a boye sunansa ya shigar da dan cikinsa kara kotun shari'ar Muslunci da ke Fagge a jihar Kano.

Rahotanni sun yi nuni da cewa mahaifin ya bukaci kotun ta daure 'dan nasa saboda ya fitine shi da masifar sace-sace da kuma shaye-shaye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel