Kotu ta yanke ma wasu masu safarar kwaya shekara 18 gidan yari

Kotu ta yanke ma wasu masu safarar kwaya shekara 18 gidan yari

- An kama wasu 'yan uwa biyu da safarar miyagun kwayoyi ba tare da bin ka'idar doka ba

- Kotu ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari shekara 18

- An kama su da mallakar kwaya mai shige da hodar Iblis

Wata Kotun koli a Abuja ta zartar wa da wasu 'yan uwa biyu shekara 18 a gidan yari bisa safarar kwaya ba.

Mai shari'a Ibrahim Auta ya kama Chukuwa Ugbai dan shekara 31 da dan uwansa Robert Ugbai mai shekara 49 da laifin sayar da miyagun kwayoyi. Wannan dalilin ya sa ya zarce musu hukuncin shekara 10 da 8 ga dan uwan a gidan yari.

Kotu ta yanke ma wasu 'yan uwa masu safarar kwaya shekara 18 gidan yari
Kotu ta yanke ma wasu 'yan uwa masu safarar kwaya shekara 18 gidan yari

Hukumar yaki da fatauci da sarrafa miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama 'yan uwan da hadin kan aikata laifi da safarar miyagun kwayoyi da ya sabawa dokar hukumar NDLEA.

An kama su da mallakar kilo-kilon wata kwaya mai suna Cannabis Sativa, wadda take iya sa maye mai shige da Hodar Iblisa ba tare da bin ka'idar doka ba.

KU DUBA: Tafiyar Shugaba Buhari bata sabawa doka ba

Jojin ya yanke wa Chukwuka hukuncin zaman shekara 8 a bisa laifin farko da 10 goma a na biyu da aka tuhume shi da shi, haka dan uwan Robert shekara 8 a farko da 8 a karshe duk zasu yi a tare.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng