Gwamnan Arewa Ya Bayyana Hanyar da Za a Kawo Ƙarshen Tsadar Rayuwa a Najeriya
- Gwamnan jihar Jigawa ya ba 'yan Najeriya shawarar hanyar da 'yan Najeriya za su iya fita daga kangin tsadar rayuwar da ake ciki
- Umar Namadi wanda ya amince Najeriya na fama da matsin tattali, ya ce gwamnati za ta tallafawa 'yan kasar su koma gona
- Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan da Sarkin Dutse, Sarkin Dutse, Hameem Sanusi suka aika sakon barka da zuwan babbar Sallah
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Jigawa - Gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su koma noma, inda ya yi alkawarin gwamnati za ta ba da tallafi domin rage matsalolin tattalin arziki.
A cikin sakonsa na Sallah, Gwamna Umar Namadi ya amince da cewa akwai tarin matsaloli na tattalin arziki da kasar nan ke fama da shi.
Jigawa: An yi huduba kan zaman lafiya
Amma a rahoton TVC News, gwamnan jihar na Jigawa ya ba da tabbacin cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi suna aiki tare domin samar da mafita mai dorewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daruruwan al’ummar Musulmi daga ciki da wajen birnin Dutse ne suka gabatar da Sallar Idi tare da mai martaba Sarkin Dutse da Gwamna Umar Namadi.
Karkashin jagorancin mataimakin babban limamin masallacin Dutse, Sheikh Musa Bala, an jaddada muhimmancin zaman lafiya, kaunar juna da tsaftar muhalli.
Gwamna ya fadi hanyar rage talauci
Gwamna Umar Namadi da Mai Martaba Sarkin Dutse Hameem Nuhu sun taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Sallah ta bana.
Gwamna Namadi ya nanata mahimmancin ‘yan kasa su koma noma, inda ya yi alkawarin ba 'yan jihar goyon bayan gwamnati a fannin, in ji rahoton Independent.
Ya kuma jaddada bukatar samar da abinci wanda zai wadaci al'uma, cire su daga kangin talauci da kuma bunkasar tattalin arziki.
Sarkin Dutse Hameem Nuhu ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su rungumi dabi’ar zaman lafiya, soyayya, da karamci kamar yadda Annabi Ibrahim ya yi misali da su.
Alhazai 19 sun mutu wajen aikin Hajji
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumomin kasashen Jordan da Iran sun sanar da cewa mahajjata 19 daga kasashensu ne suka mutu a wajen aikin Hajji a kasar Saudiya.
Rahotanni sun bayyana cewa mahajjatan sun mutu ne sakamakon tsananin zarfin da ake yi a kasar, wanda aka ce ya haura zuwa digi 2 daga 1.5 a ma'aunin Celsius.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng