Gwamnati ta ware kadadar noma 500 don noman shinkafa ga matasa
- Gwamnatin jihar jigawa ta ware kadadar noma 500 domin noman shinkafa ga matasan garuruwan Kwangwara da Bakin Kuja da Giwa da kuma Jangargari a yankin karamar hukumar Birnin Kudu.
- Mataimaki na musamman ga gwamna kan noman shinkafa Alhaji Jamilu Dan Malam Jahun ya sanar da hakan a lokacin tantance matasan
Ya ce gwamnatin jiha ta yi harrow a filin tare da haka rijiyoyi yayinda ake sa ran bada injinan ban ruwa da irin shinkafa da takin zamani da matasan zasu biya bayan girbin shinkafar.
Legit.ng ta samu labarin cewa a jawabinsa shugaban kwamatin riko na yankin Mallam Adamu Garba ta hannun shugaban sashen aikin gona Alhaji Nasuru Abubakar ya yabawa gwamnatin jiha bisa bullo da shirin tare da bada tabbacin karamar hukumar na marawa shirin baya.
KU KARANTA: Manjo Almustapha ya kafa sabuwar jam'iyya
A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya karkashin hukumar nan mai kula da ilimin bai daya ta UBEC za ta samar da littattafan a dukkanin makarantun firamare na kasa a watan shida na wannan shekara ta 2017.
Babban sakataren hukumar UBEC na kasa Dakta Hamid Boboyi, shine ya tabbatar da haka, inda yake cewa, gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta himmatu wurin inganta harkan ilimi a kasar nan.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Nan ma matasa ne ke tsokaci game da tsadar abinci
Asali: Legit.ng