Gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa manoma 50,000 tallafi

Gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa manoma 50,000 tallafi

- Gwamnatin jihar Jigawa zata bayar da tallafi ga manoma 50,000 a jihar karkashin shirin Fadama III

- Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da ofishin na shirin Fadama III a garin Dutse

- Kwamishinan noma a jihar ya kuma bayyana cewa manoma 7,255 ne suka sami tallafi domin noman rani a bana

Gwamnatin jihar Jigawa zata bayar da tallafi ga manoma 50,000 a karkashin tsarin ta na noman cluster. Gwamna Muhammadu Badaru ne ya bayyana hakan a taron kaddamar ta ofishin Fadama III da kuma raba wa manoma kayayakin aiki a ranar Alhamis a Dutse.

Gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa manoma 50,000 tallafi
Gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa manoma 50,000 tallafi

Gwamna Badaru, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, Alhaji Ibrahim Hadejia ya kara jadada cewa noma yana daya daga cikin ababen da gwamnatin jihar ta fi mayar da hankali a kai, hakan yasa dole a taimaka wa kungiyoyin na manoma.

DUBA WANNAN: Dan kunar bakin wake ya kashe mutum 6 a kasuwar Borno

Kwamishinan noma na jihar, Alhaji Kabiru Ali ya mika godiyar sa ga gwamnan bisa yadda ya ke baiwa harkar noma mahimmanci, ya kuma kara da cewa manoma 7,255 ne suka sami tallafi domin noman rani a bana.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kashe kudi har naira miliyan 140 domin taimakawa manoma 350 a karkashin shirin na Fadama III.

Jagoran shirin Fadama III a jihar na Jigawa, Alhaji Aminu Isa ta mika godiyarsa ga gwamnatin jihar domin goyon baya da take baiwa shirin a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel