Ana Kukan Rashin Kudi, Gwamnan Kaduna Yana Kashe N4bn a Ciyar da Dalibai

Ana Kukan Rashin Kudi, Gwamnan Kaduna Yana Kashe N4bn a Ciyar da Dalibai

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana yadda ta ke kashe mukudan kudi domin ciyar da ɗalibai da suke wasu makarantu a faɗin jihar
  • Mai taimakawa gwamna kan ciyar da ɗalibai, Dakta Fauziyya Ado ce ta fitar da rahoton ga manema labarai a jiya Lahadi
  • Dakta Fauziyya Ado ta bayyana yadda shirin ciyar da ɗalibai a jihar ke kara saka yara shiga makarantu da kuma haɓaka tattali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna karkashin gwamna Uba Sani ta fitar da rahoto kan kudin da ta ke kashewa wajen ciyar da ɗalibai.

Mai taimakawa Mai girma Uba Sani kan harkokin ciyar da yan makaranta, Dakta Fauziyya Ado ce ta bayyana adadin kudin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Gwmana Uba Sani
Kaduna na kashe N4b wajen ciyar da 'yan makaranta duk shekara. Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Dakta Fauziyya Ado na cewa shirin ciyar da ɗalibai a makarantun yana kawo cigaba a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makarantun da ake ciyar da ɗaliban Kaduna

Mai taimakawa Uba Sani kan harkokin ciyar da ƴan makaranta, Dakta Fauziyya Ado ta ce akwai makarantun kwana 51 a jihar Kaduna da suke cin moriyar shirin.

Dakta Fauziyya Ado ta ce makarantun kwanan suna cikin daukacin kananan hukumomin jihar guda 23.

Yadda ake kashe N4b ga daliban Kaduna

Har ila yau, Dakta Fauziyya Ado ta bayyana cewa a cikin makarantun kwana 51 da ke jihar akwai ɗalibai sama da 25,000.

Mai taimakawa gwamnan ta ce adadin daliban suna lakume kudi kimanin N4b duk shekara wajen ciyar da su da ake a zangon karatu uku, rahoton jaridar Leadership.

Fa'idar ciyar da ɗalibai a makarantu

Kara karanta wannan

Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta kama 'masu saida' takardar aiki a gwamnatin jiha

Cikin bayanan da ta fitar, Dakta Fauziyya ta bayyana cewa shirin ya taimaka wajen kara adadin dalibai da suke shiga makarantun jihar.

Ta kuma tabbatar da cewa shirin yana bunkasa harkar noma da sana'ar sayar da abinci a jihar, saboda a wurarensu ake sayen kayan abinci.

Gwamnan Kaduna zai gyara asibitoci

A wani rahoton, kun ji cewa mai girma Uba Sani ya yi Allah wadai da irin mummunan halin da ya tsinci manyan asibitoci da ake da su a Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna ya ce an yi shekaru 20 ba a gyara asibitoci ba, amma ya dauki alkawarin zai gyara matsalolin domin inganta kiwon lafiya a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng