Yaron Sanusi II Yayi Magana da Kotu Ta Saurari Shari’ar Aminu Ado Bayero
- Ashraf Sanusi Lamido Sanusi ya yi tsokaci a lokacin da ake shari’a da gwamnatin jihar Kano a kan rikicin masarauta
- Yaron Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana ganin babu ta inda gwamnati ta toye hakkin Alhaji Aminu Bayero bayan tsige shi
- Bayan an gama sauraron kowane bangare a shari’ar, an yi hukuncin da ya sabawa tunanin Ashraf Sanusi Lamido Sanusi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Bayan tsawon lokaci ana jiran kotu ta yi hukunci, a karshe alkali ya kawo karshen rikicin masarautar Kano.
Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya kalubalanci sauke sarki Aminu Ado Bayero daga karaga.
Ashraf Sanusi II a kan rikicin sarautar Kano
Ashraf Sanusi Lamido Sanusi ya tofa albarkacin bakinsa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter bayan an yi hukunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Ashraf Sanusi Lamido kamar yadda ya saba, ya tsoma baki a shari’ar da za a iya cewa babu wanda ya yi nasara.
Duk da kotu ta ce ta na da hurumin sauraron karar, Aminu Ado Bayero, da alama dai Ashraf yana da ja a kan matsayar.
Yaron Sarkin ya nuna cewa ba a toyewa Alhaji Aminu Ado Bayero hakkin zama ‘dan kasa ba dominyin sarauta gata ce.
Ashraf: "Ba a toyewa Aminu Ado hakki ba"
“Ko mutum bai je makarantar koyon shari’a ba, ya san babu wani ‘hakki’ a zama Sarki.”
“Akwai hakkokin rayuwa, tunani, yawo da sauransu, wadannan su ne ainihin hakkoki,”
“Kuma a cikinsu babu wanda aka toye masa (Mai martaba Aminu Ado Bayero).”
- Ashraf Sanusi Lamido
Sarki Aminu Ado a fadar Nassarawa
A zancen da ya yi a shafinsa, Ashraf Sanusi ya yi magana a kaikaice game da fadar Nasarawa da basaraken yake zama.
Abin da ya ke nema ya nuna shi ne Sarkin Kano na 15 ya shiga hurumin da ba na shi ba.
A karshe alkali ya ci gwamnatin Kano tarar N10m kan take hakkin Aminu Ado Bayero wajen maido Muhammadu Sanusi II.
Babu mamaki Ashraf wanda ma’aikacin banki ne kuma masani a ilmin tattalin arziki bai yi tunanin haka shari’ar za ta kaya ba.
Sanusi II ya soki gwamnatin Ganduje
Ana da labari cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya zargi gwamnatin Dr. Abdullahi U. Ganduje da raba kan gidan dabo.
Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ce ana zaune kurum gwamnatin jihar Kano ta kirkiro masarautu, ta lalata tarihin kasar.
Asali: Legit.ng