Rayuwar Tinubu Za Ta Iya Shiga Hadari, Majalisa Ta Nemi a Siya Masa Sabon Jirgi
- Gwamnatin Najeriya na shan suka kan yadda majalisa ta bayyana bukatar a siyo sabbin jirage ga shugaban kasa da mataimakinsa
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke fuskanar bakar wahalar tattalin arziki da karyewar darajar Naira
- Ana fargabar rashin siyan jiragen zirga-zirga ga fadar shugaban kasa kan iya jefa rayuwar Tinubu da Shettima a hadari
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Tsaro da Leken Asiri ya goyi bayan kiran da Majalisar Wakilai ta yi na sayen sabbin jiragen sama ga Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kasheem Shettima.
Shugaban Kwamitin, Shehu Umar ne bayyana hakan yayin da yake zantawa da PREMIUM TIMES a daren Asabar daga Saudiyya, inda yake gudanar da aikin hajjin bana.
Ya bayyana cewa rashin gaggauta sabunta jiragen saman fadar shugaban kasa na iya jefa rayukan Shugaba Tinubu da mataimakinsa cikin hadari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai bukatar kare rayuwar Tinubu da Shettima
A wani rahoto da aka tura fadar shugaban kasa, kwamitin na majalisa ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta sayen jirage biyu domin Shugaba Tinubu da Shettima domin tabbatar da tsaron manyan jami’an kasar.
Kiran da kwamitin majalisar ya yi nan take ya jawo suka daga wasu ‘yan Najeriya da ke kalubalantar hikimar sayen sabbin jiragen sama a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsananciyar wahalar tattalin arziki.
Majalisa ta fadi dalilin nemawa Tinubu sabon jirgi
Sai dai da yake magana kan wannan batun a ranar Asabar, Malam Umar ya ce:
"Kun ga rahoton kwamitin ne? Shawarwarin kwamitin a bayyane suke a fili. Domin cimma wadannan shawarwari, kwamitin ya gudanar da zaman sauraron bincike kuma ya tattauna da jami'an jiragen saman fadar shugaban kasa.”
Ba wannan ne karon farko da ‘yan Najeriya ke nuna damuwa kan bukatun tafiyar da mulki a kasar ba, hakan ya sha aukuwa a baya, kuma ba a cika maida hankali ga kokensu ba.
Yadda Tinubu ya ci dungure a bikin ranar dimokradiyya
A baya kadan, shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zamewar da ya yi har ya fadi kasa a lokacin da zai hau mota a filin Eagle Square ranar Laraba.
Idan ba ku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda Tinubu ya zame a lokacin da yake kokarin hawa motar faretin bikin ranar dimokuradiyya.
Bayan faruwar lamarin, kafafen sada zumunta suka hargitse da mayar da martani, inda mutane suka rika tofa albarkacin bakinsu kan faduwar Tinubu.
Asali: Legit.ng