Aminu Ado Bayero Ya Aika da Muhimmin Sako Ga Tinubu da Gwamna Abba

Aminu Ado Bayero Ya Aika da Muhimmin Sako Ga Tinubu da Gwamna Abba

  • Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi jawabi domin murnar zuwan lokacin bukukuwan babbar Sallah
  • Mai martaba sarkin ya taya shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar zuwan lokacin Sallah
  • Aminu Ado Bayero ya kuma bayyana cewa ya fasa yin hawan Sallah ne domin a samu ɗorewar zaman lafiya a jihar bayan jami'an tsaro sun ba da shawarar a yi hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya taya shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar bukukuwan Sallah.

Sarkin ya kuma sanar da cewa an dakatar da gudanar da hawa da aka shirya tun da farko biyo bayan shawarwarin da jami’an tsaro suka bayar domin a ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC ya fallasa wanda ya jawo ake binciken gwamnatin El-Rufai

Aminu Ado Bayero ya taya Bola Tinubu murnar zuwan Sallah
Aminu Ado Bayero ya fasa hawan Sallah a Kano Hoto: Kamfa_emirate_photography
Asali: Facebook

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a fadar sarki da ke Nassarawa ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane saƙo Aminu Ado Bayero ya ba da?

"A wannan rana da dukkan musulmi muminai suke raya ranar Arafah, muna taya kowa murna a wannan muhimmin lokaci."
"Domin haka muna taya shugaban ƙasa da gwamna barka da Sallah kuma muna addu’ar Allah ya ba su ƙwarin gwiwar sauke nauyin da ke kansu."
"Muna kira a gare su da su ci gaba da kawo romon dimokuraɗiyya ga jama'a, kare rayukansu da dukiyoyinsu, sannan muna kira ga jama'a da su yiwa shugabanninsu addu'a."
"Mun ɗage dukkanin hawa biyo bayan shawarar da jami'an tsaro suka ba da domin samun ɗorewar zaman lafiya."

- Alhaji Aminu Ado Bayero

A halin da ake ciki, Sarkin Dawaki, Aminu Babba Dan Agundi ya sanar da cewa Sarkin zai yi sallar Idi a fadar ta Nasarawa da misalin ƙarfe 8:00 na safe.

Kara karanta wannan

Bayan rasa mulkin Kano, a ƙarshe, Tinubu ya naɗa Nasiru Gawuna mukami

Ƴan sanda sun hana hawa a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta haramta yin hawa a yayin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah mai zuwa a jihar.

Rundunar ta bayyana cewa a yayin bikin babbar Sallah na bana, ba za a yi hawan Sallah ba kamar yadda aka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel