Hawan Sallah: 'Yan Sandan Kano Sun yi Bayani kan Wasikar Sarki na 15, Aminu Bayero

Hawan Sallah: 'Yan Sandan Kano Sun yi Bayani kan Wasikar Sarki na 15, Aminu Bayero

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta musanta cewa ta karbi takarda daga sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero domin samar da tsaro yayin hawa a bukukuwan sallah babba da sarkin zai yi
  • Tun da fari dai bangaren sarki Bayero ya ce an aika takarda neman tsaro a hawan sallah ga rundunar ‘yan sandan kuma tuni aka buga masu hatimin karbarta
  • Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Muhammad Usaini Gumel ya musanta cewa rundunar ta karbi takardar, inda ya kara da cewa babu wata hukumar tsaro da aka ba wa takarda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Rundunar ‘yan sanda ta musanta karbar wasikar sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero kan neman tsaro domin gabatar da bikin hawan sallah babba.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Masarautar tsagin Aminu Bayero da gwamnatin Kano ta tsige ce ta tabbatar da cewa ta aika wasika ga rundunar ‘yan sanda, kuma mataimakin kwamishina a bangaren aikace-aikace, Ahmed Umar Chuso ya buga hatimin karbarta a madadin kwamishina.

Yan sanda
Rundunar 'yan sanda ta musanta karbar takardar sarkin Kano na 15, Aminu Bayero Hoto: SP Abdullahi Kiyawa
Asali: Facebook

A wani labari da ya kebanta da Punch News, rundunar ‘yan sandan ta musanta cewa ta karbi wata takarda kamar yadda masarautar ta fada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba mu karbi takardar Sarki ba,” Gumel

Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana cewa babu wanda ya aika masu da takarda kan neman tsaro da bikin hawan sallah babba da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya umarci jama'arsa su yi.

Wannan na zuwa ne bayan fadar sarki ta Nassarawa ta umarci dukkanin hakimai, dagatai da masu unguwanni su fito fadar domin karbar umarni kan bikin hawan sallah, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Sarkin Kano na 15 ya rubuta takarda ga ƴan sanda kan hawan sallah

A wani sakon kar-ta-kwana, kwamshinan ‘yan sanda a Kano, CP Muhammad Usaini Gumel ya ce ba a sada rundunar ‘yan sandan Kano ko wata hukumar tsaro a jihar da takarda makamanciyar wannan ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa ana so ayi amfani da batun takardar ne domin yada jita-jita a jihar Kano yayin da ake ci gaba da dambarwa masarautar jihar.

Sarki na 15 ya rubuta takarda ga ‘yan sanda

A baya mun kawo labarin cewa fadar sarkin Kano ta 15 da ke Nassarawa ta rubuta wasika ga rundunar ‘yan sandan Kano domin samar da tsaro yayin hawan bukukuwan sallah.

Tun a ranar Talata ne masarautar ta umarci masu rike da sarautun gargajiya su fito da dawakai domin shiga birni a gudanar da hawan sallah duk da cewa gwamnatin Kano ta tube rawanin Bayero.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.