Bayan Dikko Radda Ya Buɗe Kofa, Gwamna a Arewa Ya Ba Ma'aikata N10,000 Goron Sallah
- Yayin da ake shirin gudanar da bukukuwan babbar Sallah, Gwamna Bala Mohammed ya tallafawa ma'aikatan jihar Bauchi
- Gwamnan ya raba kyautar N10,000 ga dukkan ma'aikatan jihar domin gudanar da bukukuwan salla cikin walwala
- Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar da safiyar yau Asabar 15 ga watan Mayu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya gwangwaje ma'aikata a jihar da abin alheri.
Bala ya raba kyautar N10,000 ga duka ma'aikatan jihar domin gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala.
Sallah: Bala Mohammed ya tallafawa ma'aikata
Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook da safiyar yau Asabar 15 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Bala ya ce ya yi hakan ne domin ragewa jama'a halin da suke ciki ganin yadda ake fama da tsadar rayuwa.
"Lura da halin ƙunci da tsadar rayuwa da muka tsinci kanmu a ciki a wannan lokaci da muke shirin bikin Sallah, na amince da biyan tallafin dubu goma-goma ga ɗaukacin ma’aikata."
"Na dauki wannan matakin ne domin rage raɗaɗin da mutane ke ciki."
- Bala Mohammed
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta gajiya ba wurin rokon al'ummar jihar addu'o'i domin samun zaman lafiya.
Gwamna Bala ya bukaci addu'o'i daga al'umma
"Ba za mu gajiya ba wajen kira ga al’umma da su sanya jihar Bauchi da kuma Najeriya cikin addu’oinsu domin samun zaman lafiya da haɓakar tattalin arziki."
"Kada mu manta da tallafawa marasa ƙarfin cikin mu yayin bukukuwan Sallah."
- Bala Mohammed
Gwamnan a karshe, ya yi addu'ar neman yardar ubangiji da amsar ibadun da ake yi.
Radda ya gwangwaje ma'aikata a Katsina
Kun ji cewa Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya tallafawa ma'aikatan jiharsa da goron sallah.
Radda ya ba ma'aikata kyautar N15,000 domin gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala tare da bashin N30,000.
Asali: Legit.ng