Bayan Hana Hawan Sallah, NSCDC Ta Dauki Kwakkwaran Mataki Awanni Kafin Idi a Kano

Bayan Hana Hawan Sallah, NSCDC Ta Dauki Kwakkwaran Mataki Awanni Kafin Idi a Kano

  • Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin dakile dukkanin barazanar tsaro da za a iya fuskanta da bukukuwan sallah babba a Kano
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar ya tabbatarwa da Legit Hausa cewa za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro kamar KAROTA da hukumar tsaron farin kaya
  • Sauran hukumomin da za su yi aiki a Kano sun hada da rundunar 'yan sanda, hukumar FRSC domin kare afkuwar hadurra a kan hanya duk a domin ganin an yi bukukuwan sallah lafiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta bayyana kammala shirye-shiryen tabbatar da tsaron dukiya da rayukan jama’a a domin gudanar da bikin sallah babba a Kano.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashin da ya sace dabbobi, ya kalmashe kudin mutane a aljihu

NSCDC ta shaida cewa ta baza jami’anta akalla 3,168 a sassan Kano domin ganin jama’asun bi doka da oda yayin shagulgulan sallah babba, yayin da jihar ke cikin yanayin dambarwar masarauta.

NSCDC
Hukumar NSCDC ta baza tsaro a Kano gabanin sallah Hoto: @Official_NSCDC
Asali: Twitter

Leadership News ta wallafa cewa jami’in hulda da jama’a na hukumar a Kano, Ibrahim Abdullahi ne ya tabbatar da shirin da su ke yi na tsaron al’umma domin gudanar da shagulgulan sallah lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu na aiki da hukumomin tsaro," NSCDC

Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta ce za ta yi aikin hadin gwiwa da sauran jami'an tsaro a Kano yayin bukukuwan sallah babba a loko da sakon jihar. Punch News ta wallafa cewa hukumar za ta yi aiki da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa a Kano (KAROTA), DSS, FRSC da 'yan sanda wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Katsina: Hisbah ta garkame otal da ya saba alkawari, ana zargin badala da 'yan mata

Da ya ke zantawa da Legit Hausa ta wayar tarho, kakakin hukumar, Ibrahim Abdullagi ya bayar da tabbacin za su kare dukiya da rayukan jama'a yayin bukukuwan sallah da bayanta.

Sallah: Malami ya ba musulmi shawara

A baya mun kawo muku labarin cewa wani malamin addinin musulunci Dr. Tajudeen Adebayo ya shawarci musulmi da za su yi layya a sallar bana su tuna da makotansu.

Ya bayyana haka ne yayin da ake zaton matsin rayuwa zai hana musulmin kasar nan da yawa sayen dabbar da za su yi layya da ita, lamarin da malamin ya ce ka da a shiga damuwa da yawa a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.