Sarautar Kano: Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Aminu Ado Bayero, Ta Ci Abba Tarar N10m

Sarautar Kano: Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Aminu Ado Bayero, Ta Ci Abba Tarar N10m

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, Babbar Kotun Tarayya ta ci tarar gwamnatin jihar N10m
  • Kotun ta dauki matakin ne bayan umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf na cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
  • Babbar kotun ta ce umarnin gwamnan ya sabawa sashe na 35(1) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 kan ƴancin ɗan Adam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta ci tarar gwamnatin jihar N10m kan rigimar sarauta.

Kotun ta dauki wannan matakin ne bayan gwamnatin jihar ta ba da umarnin cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Bayan yanke hukunci kan rigimar sarautar Kano, Kanawa sun tarbi Aminu Ado a faifan bidiyo

Kotu ta yi hukunci kan rigimar sarautar Kano bayan korafin Aminu Ado
Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano N10m kan tauye hakkin Aminu Ado Bayero. Hoto: @Kyusufabba, @Imranmuhdz.
Asali: Twitter

Kotu ta yi hukunci kan sarautar Kano

Hakan a cewar kotun ya saba dokar ƴancin ɗan Adam na yawo da zirga-zirga kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari’a Simon Amobeda ya yanke wannan hukunci ne kan karar da Aminu Ado ya shigar na neman kare hakkinsa na dan Adam da kuma na walwala.

Hakan ya biyo bayan umarni daga gwamnatin jihar na cafke Aminu Ado kan zargin neman ta da zauna tsaye a jihar.

Kotun ta ce umarnin cafke Aminu Ado ya saba sashe na 35(1) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

Kotu ta ci tarar Abba Kabir N10m

Ta ce matakin ya take masa hakkin zirga-zirga da kuma tilasta killace shi a gida sabanin sauran ƴan kasa saboda umarnin cafke shi da aka bayar.

Daga bisani kotun ta bukaci gwamnatin jihar ta biya Aminu Ado diyyar N10m saboda take masa hakkinsa na ɗan kasa.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: 'Yan sanda sun dauki mataki kan hawan Sallah a Kano

Kotun ta dakatar da kamawa ko barazana da cin mutunci ko kuma tsare Aminu Ado Bayero domin kare masa ƴancinsa na ɗan Adam.

Ta kuma yi watsi da bukatar Aminu Ado Bayero ta neman fitar da Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II daga Fadar Gidan Rumfa.

Ƴan sanda sun hana hawan sallah

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta haramta yin hawa a yayin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah mai zuwa a jihar.

Rundunar ta bayyana cewa a yayin bikin babbar Sallah na bana, ba za a yi hawan Sallah ba kamar yadda aka saba.

Kwamishinan ƴan sandan a jihar, CP Usaini Gumel shi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, 13 ga watan Yunin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.