Badaƙalar N1.85bn: Kotu Ta Tasa Ƙeyar Jami’an Gwamnatin Tarayya Zuwa Gidan Yari
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta iza keyar wasu jami'an gwamnatin tarayya guda biyu zuwa gidan gyaran hali
- An ce kotun ta ba da umarnin tsare jami'an a kurkuku bayan da hukumar ICPC ta gurfanar da su kan tuhumar zambar N1.85bn
- Suna daga cikin jami’an hukumar kula da ayyukan wutar lantarki a yankunan karkara da ICPC ke zargi da wawurar kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin tsare wasu jami’an hukumar kula da ayyukan wutar lantarki a yankunan karkara.
An gurfanar tare da garkame Emmanuel Pada da Umar Laraye bisa zargin almundahanar Naira biliyan 1.85.
Suna daga cikin jami’an hukumar REAhudu da hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta gurfanar kan zargin zambar N1.85bn in ji rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudin da ake zargin jami'an sun wawure
Sauran jami’an biyun da ke fuskantar tuhume-tuhume daban-daban, su ne Henrietta Okojie (wadda za a gurfanar a yau Juma’a) da kuma Usman Kwakwa, wanda tuni aka gurfanar da shi.
Yayin da ake tuhumar Kwakwa da zambar N1.853bn; An zargi Karaye da karkatar da N165m; Ana zargin Okoje ya wawure N342m yayin da Titus ya yi awon gaba da N261m.
Jaridar Vanguard ta ruwaito Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin a tsare Pada da Laraye a gidan yari jim kadan bayan gurfanar da su a ranar Alhamis.
Yadda ake zargin sun yi zambar kudin
A cikin tuhume-tuhumen, ICPC ta zargi Titus da damfarar REA har N261m ta hanyar yin “karyar zai kai ziyarar sa ido a kan wasu ayyuka.”
Shi kuma Karaye ana zarginsa da karkatar da N165m ta hanyar fitar da kudi daga lalitar gwamnati karkashin tsarin biyan kudi na GIFMIS da sunan zai je ziyarar ayyuka a 2023.
Dangane da Okojie, ICPC ta yi zargin cewa ya karkatar da N342m 'da sunan zai je ziyarar ayyuka" wanda ya karya dokar zamba da sauran laifuffuka ta 2006.
Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin $2.25bn
A wani labarin, mun ruwaito cewa Bankin Duniya ya ce ya amince zai ba Najeriya tallafin bashin dala biliyan 2.25 domin farfado da tattalin arzikinta.
Da ya ke tsokaci a kai, ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya ce tallafin bankin duniyan zai taimaka wajen aiwatar da kasafin kudin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng