EFCC Ta Gurfanar da Jami'an Gwamnati 5 Bisa Cinye Kudin Fanshon Malaman Firamare

EFCC Ta Gurfanar da Jami'an Gwamnati 5 Bisa Cinye Kudin Fanshon Malaman Firamare

  • EFCC ta ce ta gurfanar da wasu jami'an gwamnatin jihar Sokoto bisa zargin cinye kudin fansho
  • An gurfanar da jami'an 5 bayan yawan korafe-korafe kan cewa sun cinye kudin fanshon malaman Firamare
  • Duk da cewa basu amsa laifinsu ba, za a ci gaba da sauraran kara don tantance gaskiyar lamarin

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta tabbatar da gurfanar da wasu jami'an Hukumar Fansho ta Makarantun Firamare na Jihar Sokoto a gaban Mai Shari'a Muhammad na Babbar Kotun Jihar.

An tattaro cewa, wadanda ake zargin suna fuskantar tuhume-tuhume 27 da suka hada da hadin baki, coge, cin amana da kuma karkatar da kudade N553,985,624, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Daraktan Kudi, Hassana Moyi; Sakatare, Abubakar Aliyu; Mataimakin Darakta, Halliru Ahmed; Akawun hukumar, Kabiru Ahmed da Dahiru Muhammad Isa, mai karbar kudi na hukumar.

KARANTA WANNAN: Muhimman Abubuwa 6 da Ya Kamata Ku Sani Game da Nnamdi Kanu Shugaban IPOB

EFCC Ta Gurfanar da Jami'an Gwamnatin Sokoto 5 Bisa Cinye Kudin Fanshon Malaman Firamare
Alamar hukumar EFCC | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A shekarar 2019, EFCC ta karbi korafe-korafe daga dimbin ‘yan fanshon makarantun firamare da ke korafin cewa har yanzu ba a ba su alawus dinsu ba tun da suka yi ritaya.

EFCC ta ce jami'an sun aikata laifin cin amana ne wanda ya saba da sashi na 311 na dokar Penal Code Law CAP 89, dokokin Arewacin Najeriya kuma za a hukunta su a karkashin Sashe na 312 na wannan dokar.

Wadanda ake tuhumar sun ki amincewa da laifunsa lokacin da aka karanta tuhumar da ake musu.

Lauyan da ke gabatar da kara, S. H. Sa’ad, ya roki kotun da ta sanya ranar fara shari’ar tare da hanzarta sauraran karar.

A.Y. Abubakar, lauyan da ke kare wanda ake kara, ya gabatar da bukatar neman a ba shi belinsu.

Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin cewa hukumar za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.

Kalu, wanda yanzu haka dan majalisar dattijai ne, Kotun Koli ta sake shi a kan ka'idoji bayan an same shi da laifin satar biliyoyin nairori lokacin da yake gwamnan jihar Abia tsakanin 1999-2007.

KARANTA WANNAN: Badakalar Tinubu: EFCC ta ce tana ci gaba da bincikar shugaban APC Tinubu

Bayan Shekaru 6, Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar EFCC

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin George Abangeekpungu a matsayin sakataren hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC).

Nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ofishin babban lauyan Najeriya da ma'aikatar shari'a ta kasa, Umar Jibrila Gwandu ya sanyawa hannu a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewar sanarwar, wa'adin sabon nadin zai kasance na shekara biyar ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.