'Yan sanda sun gurfanar da jami'an gwamnati da wata 'yar kasuwa da suka saci tallafin COVID-19

'Yan sanda sun gurfanar da jami'an gwamnati da wata 'yar kasuwa da suka saci tallafin COVID-19

- An gurfanar da wasu jami'an gwamnatin jihar Oyo a kotu kan zargin satan tallafin Korona

- Wadanda ake zargin sun saci buhuhunan sikarin Dangote mallakar jihar har guda 40

- An gurfanar dasu tare da matar da ta sayi kayan satan ido rufe da sanin kayan gwamnati ne

Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu jami’an Gwamnatin Jihar Oyo biyu a gaban wata Babbar Kotun Majistare, da ke Ibadan, The Punch ta ruwaito.

An gurfanar dasu ne bisa zargin sata da sayar da buhunan sukari 40 daga tallafin COVID-19 na jihar.

An kuma gurfanar da wata 'yar kasuwa da ake zargi da sayar da kayan satar ga Kafayat Babalola tare da jami'an gwamnati.

An tuhumi jami’an da 'yar kasuwar da laifin hadin baki, sata, da karbar kayan sata.

KU KARANTA: Kanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota

'Yan sanda sun gurfanar da jami'an gwamnati da wata 'yar kasuwan suka saci tallafin COVID-19
'Yan sanda sun gurfanar da jami'an gwamnati da wata 'yar kasuwan suka saci tallafin COVID-19 Credit: Premium Times
Asali: Facebook

Wadanda ake tuhumar sun hada da direba mai shekaru 50, Adebiyi Azeez, da kuma Sunday Akinleye, mai shekaru 43 kuma mataimakin jami’in kula da kayan tallafin a ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu.

Mai gabatar da kara, Sunday Ogunremi, ya fadawa kotun cewa an aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Disamba.

Ya ce, “Adebiyi da Akinleye sun saci buhu 40 na sikarin Dangote, wanda darajarsu ta kai N60,000 na tallafin COVID-19 kuma mallakar Gwamnatin Jihar Oyo.

“Su biyun sun yi amfani da motar hukuma ta Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarauta wajen kai kayan ga mai saye.

KU KARANTA: Kwastam ta jaddada hana shigo da shinkafa

"Wanda ake kara na uku, Misis Kafayat Babalola, 'yar kasuwa a kasuwar Agbeni, Ibadan, ta karbi buhunan sikari 40 din, da sanin cewa ba na sayarwa ba ne, mallakar gwamnatin jihar ne."

Ya ce laifin ya ci karo da sashi na 516, 390 (9) da 427 na kundin manyan laifuka na jihar Oyo, 2000.

Wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.

Alkalin Kotun, Mista Taiwo Oladiran, ya ba da belin su kan kudi N20,000 kowannensu, tare da masu tsaya musu mutum biyu kowannensu a kwatankwacin wannan kudin, sannan ya daga karar zuwa ranar 8 ga Fabrairu don sauraro.

A wani labarin daban, Masana ilimin Kawayar Cuta sun shawarci Gwamnatin Tarayya game da sayen maganin rigakafin COVID-19 a wannan lokacin, suna masu cewa ba shi da bukatar gabatar da shi yanzu ga ‘yan Najeriya.

Wata masaniyar kwayar cutar a Cibiyar Nazarin Likitocin Najeriya, Farfesa Rosemary Audu, a wata hira da ta yi da wakilin jaridar The Punch, ta ce ba za a bukaci allurar rigakafin ba idan kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan sun samar da kwayoyin kariya daga kwayar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.