Hukumar Yaki da Rashawa ta Kano ta Kama 'Masu Saida' Takardar Aiki a Gwamnatin Jiha

Hukumar Yaki da Rashawa ta Kano ta Kama 'Masu Saida' Takardar Aiki a Gwamnatin Jiha

  • Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta bayyana kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen sayar da takardun daukar aiki a jihar
  • Shugaban hukumar Barista Muhyi Magaji Rimingado da ya bayyana haka ya ce an fara bincike, har an gayyaci manyan sakatarorin gwamnatin jihar guda uku domin amsa tambayoyi
  • Ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ba su umarnin tabbatar da bankado wadanda ke cikin zambar dubunnan masu neman aiki a jihar tare da daukar matakin hukuntasu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta bayyana kama wasu ma’aiakatan gwamnati guda biyu da gayyatar manyan sakatarori uku domin amsa tambayoyi kan sayar da tadardun aiki ga mazauna jihar.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin-gado da ya bayyana haka ya ce an kama mutanen ne bayan gano badakala kan bayar da takardun aiki a ofishin shugaban ma'aikatan jihar.

Barr. Muhuyi Magaji Rimingado
Hukumar yaki da rashawa ta Kano ta fara binciken masu zambar daukar aiki Hoto: Barr. Muhuyi Magaji Rimingado
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa kwarya-kwaryar binciken da hukumar ta gudanar ya tabbatar masu da cewa akwai kumbaya-kumbiya a harkar raba wasu daga takardun aiki a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Ana binciken masu saida takardun aiki

Shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimingado ya ce mutanen da su ka kama kan zambatar masu neman aiki su na bayar da hadin kai.

Ya ce bincike ya na yin nisa, kuma nan gaba za a bankado wadanda ke cutar masu neman aiki a gwamnatin jihar.

”Mu na aiki tukuru domin kawar da cin hanci da tabbatar da an yi adalci ga dubunnan masu neman aiki da aka zalunta," cewar barista Muhyi Magaji Rimingado.

Kara karanta wannan

Ana shirin Babbar Sallah, gwamna ya dakatar da wasu manyan hadimai 3 daga aiki

- Muhyi Magaji Rimingado

Punch News ta wallafa cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta umarci hukumar da tabbatar da an hukunta masu sayar da takardar daukar mutane aiki a jihar.

Ana binciken almundahana kan tallafi a Kano

A wani labarin kun ji cewa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta fara binciken zargin almundahana a yanayin raba tallafin N50,000 ga masu kananan sana'o'i a titunan jihar.

Wani bidiyo ne ya nuna yadda wasu mutane da ake zargin jami'an gwamnati ne su na karbe N45,000 daga tallafi da aka raba domin bunkasa sana'ar mutanen, ana barinsu da N, 5000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.