Cikin Gaggawa: Majalisa Na Neman a Saya wa Tinubu da Shettima Sababbin Jiragen Sama

Cikin Gaggawa: Majalisa Na Neman a Saya wa Tinubu da Shettima Sababbin Jiragen Sama

  • Majalisar wakilai ta mika bukatar gaggawa na sayen sababbin jiragen sama guda biyu domin amfanin shugaban kasa da mataimakin sa
  • An ce kwamitin majalisar wakilan kan harkokin tsaron kasa da leken asiri ya mika rahoton wannan bukatar ga fadar shugaban kasa
  • A watan da ya gabata ne majalisar da Nuhu Ribadu suka gana kan halin da jiragen fadar shugaba kasar suke ciki bayan samun korafi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya da ta gaggauta sayen sabon jirgin sama wanda shugaban kasa da mataimakinsa za su rika amfani da shi.

Kwamitin majalisar kan harkokin tsaron kasa da leken tsaro ya ba da umarnin yana mai nuna cewa Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima na bukatar sabon jirgin sama.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Majalisa ta yi magana kan jirgin shugaban kasa
Abuja: Majalisar wakilai na neman a sayawa shugaban kasa sabon jirgi. Hoto: @TinubuMediaS
Asali: Twitter

Majalisa da Ribadu sun gana a Abuja

A ranar 21 ga watan Mayun 2023, jaridar Daily Trust majalisar wakilai da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, Nuhu Ribadu suka saka labule a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, an ce sun tattauna kan halin da jirgin fadar shugaban kasar ya ke ciki, wanda a baya ya tilasta Tinubu da Shettima hawa jiragen haya zuwa Saudiya da Kenya.

Jim kaɗan bayan kammala wannan ganawar, majalisar wakilan ta sanar da cewa za ta kafa kwamiti da zai yi nazarin tsanaki tare da bayar da shawarar abin da ya kamata ayi.

Majalisa ta nemi a sayawa Tinubu jirgi

A wani rahoto da jaridar Premium Times ta samu daga shugaban kwamitin tsaron kasa na majalisar, Ahmed Satomi, ya ce tuni aka mika bukatar sayen jirgin ga fadar shugaba kasa.

Kara karanta wannan

Ranar dimokuraɗiyya: Shugaba Tinubu ya yi jawabi kai tsaye ga al'umar Najeriya

Rahoton ya ce:

"Bayan nazarin da kwamitin ya yi kan rahoton halin da jirgin fadar shugaban kasa ya ke ciki, akwai bukatar a sayi karin jirage biyu domin amfanin shugaban kasar da mataimakinsa.
"Wannan matakin ne zai kare cire shakku ga abin da ka iya faruwa ga jiragen fadar shugaban kasar na yanzu, kuma hakan zai kare lafiya da rayuwar shugaban kasa da mataimakinsa."

Jirgin Kashim Shettima ya samu matsala

A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ya fasa tafiyar da aka tsara zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Amurka.

An bayyana cewa mataimakin shugaban ƙasar wanda tun asali aka tsara zai wakilci Tinubu a taron ba zai samu zuwa ba saboda matsalar da jirginsa ya samu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.