Sanusi II vs Aminu Ado: 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki Kan Hawan Sallah a Kano

Sanusi II vs Aminu Ado: 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki Kan Hawan Sallah a Kano

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samar da sabuwar doka kan rikicin masarautar da ake yi a jihar tsakanin Sarkin Kano na 15 da Sarkin Kano na 16
  • Rundunar ƴan sandan ta hana ɓangarorin biyu gudanar da hawa a yayin bukukuwan babbar Sallah da ke tafe
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da hakan ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin wanzar da zaman lafiya a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta haramta yin hawa a yayin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah mai zuwa a jihar.

Rundunar ta bayyana cewa a yayin bikin babbar Sallah na bana, ba za a yi hawan Sallah ba kamar yadda aka saba.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun mayar da martani, sun halaka ƴan bindiga da yawa a Arewa

'Yan sanda sun hana hawan Sallah a Kano
'Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Hoto: Kano State Police Command
Asali: Facebook

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, 13 ga watan Yunin 2024, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka hana hawan Sallah a Kano?

CP Usaini Gumel ya bayyana cewa, dokar ta zama wajibi domin wanzar da zaman lafiya tare da haɗin gwiwar dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a jihar, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

"An sanya dokar haramci kan dukkanin ɓangarorin biyu, an hana su gudanar da hawa domin bikin babbar Sallah mai zuwa."
"A wannan lokacin mai wuya, ƴan sanda za su tabbatar da umarnin kotu da ke akwai kan ɓangarorin biyu dangane da rikicin masarautar Kano, sannan tana roƙonsu da su nisanci juna tare da mutunta umarnin kotu."

- CP Usaini Gumel

Wace shawara ƴan sanda suka ba da?

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar 'yan sanda ta cafke rikakkun 'yan damfara, an kwato kayan aiki

Sai dai, kwamishinan ya shawarci jama'a da su gudanar da Sallar Idi a wuraren da ake gudanarwa kamar yadda aka saba yi a baya.

CP Usaini ya bayyana cewa rundunar ƴan sandan za ta so ci gaba da samun haɗin kai daga dukkanin masu ruwa da tsaki domin samar da cikakken tsaro a jihar.

Kano: Aminu Ado zai yi hawan Sallah

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya rubuta takarda ta musamman ga kwamishinan ƴan sanda a jihar kan shirinsa na yin hawan Sallah.

Aminu Ado Bayero ya rubuta takardar ne domin neman gudunmawar tsaro daga wajen ƴan sanda yayin bukukuwan babbar Sallah da za a yi a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng