Ana Shirin Bikin Sallah, Tsofaffin Ma'aikatan KEDCO sun Rufe Kamfanin a Kano

Ana Shirin Bikin Sallah, Tsofaffin Ma'aikatan KEDCO sun Rufe Kamfanin a Kano

  • Manyan ma'aikatan kamfanin rarraba hasken wutar lantarki a Kano, Katsina da Jigawa (KEDCO) sun tsunduma zanga-zanga sai baba ta gani bisa zargin keta hakkokinsu
  • A yau suka shiga zanga-zanga tare da rufe ofishin hukumar a Kano tare da hana kowa shiga, sun ce yajin aikin ya zama dole saboda hukumomin KEDCO sun hana su hakkokinsu
  • Tsofaffin ma'aikatan karkashin kungiyar SSAEAC sun ce mahukuntan KEDCO sun rike kudin fanshon ma'aikata da aka yi watanni 79 ana cira, da kuma tilasta masu aiki a yanayi mara dadi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Kungiyar manyan ma’aikatan samar da wtar lantarki ta SSAEAC ta fusat saboda rike hakkokinsu da kamfanin ya yi, wanda ya sa suka tsunduma zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a Ado Bayero Mall a Kano, har yanzu ana kokarin kashe wutar

A yau ne tsofaffin ma’aikatan su ka rufe ofishin kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ta KEDCO da ke Kano su na tunatar da kamfanin ya biya su hakkokinsu da ya rike.

Jihar Kano
Ma'aikata sun rufe ofishin KEDCO a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Daily Trust ta wallafa cewa ma’aikatan hasken wutar sun bayyana cewa za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani har sai an biya masu bukatunsu tare da warware dukkanin matsalolin da su ka zo da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Dole mu ka tsunduma yajin aiki,” SSAEAC

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya wayi gari da yajin aikin ma’aikatansa da su ka ce sun tsunduma yajin aiki saboda hanasu hakkokinsu.

Shugaban hukumar, Rilwan Shehu ya shaidawa manema labarai cewa dole ce ta sa suka shiga yajin aikin saboda matakin da kamfanin ya dauka kan bukatunsu.

Rilwan Shehu ya kara da cewa kamfanin ya ki amincewa da yarjejeniyar da su ka cimma da mahukunta KEDCO kan biyan bukatunsu da sakin hakkokinsu.

Kara karanta wannan

Yan sanda a Legas sun damke fasinjan da ya yi yunkurin kwacen mota

Abubuwan da suka tunzura ma'aikatan KEDCO

Daga hakkokinsu da ma’aikatan su ke nema KEDCO ta biya akwai biyan kudin fansho da aka rika gutsura daga albashin ma’aikatan na watanni 79 da kin biyan kudinsu na PAYE na watanni 80.

Haka kuma ma’aikatan sun zargi kamfanin da kin samar da wurin aiki mai kyau ga ma’aikata, rashin kayan aiki da kin biyan kudin kamala aiki ga ma’aikatan da su ka gama aiki da kamfanin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka fusatattun ma’aikatan sun rufe kofar shiga kamfanin KEDCO, sun hana kowa shiga ballantana su fara aiki.

Kamfanin KEDCO ya yanke wutar asibiti

A wani labarin kun ji cewa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya yanke wutar asibitin Imamu Wali yayin da marasa lafiya, ciki har da masu haihuwa su ke kwance.

Duk da kamfanin ya bayyana cewa ya yanke wutan ne saboda rashin biyan kudi da asibitin ke yi, gwamnatin Kano ta musanta hakan, inda ta ce ta na biyan N300,000 duk wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.